Malamai 3 na jihar Legas sun cinye kyautar shugaban kasa ta kwazon aiki

Malamai 3 na jihar Legas sun cinye kyautar shugaban kasa ta kwazon aiki

Wasu malaman makaranta uku na jihar Legas, Elusaki Iyabo, Ikuseyidunmi Pius da kuma Adeniyi Oluwasegun, sun lashe kyautar shugaban kasa ta bana ta kwazon malamai da makarantu mai sunan PTSEA, President’s Teachers and Schools Excellence Award.

Rahoton na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar ilimi na jihar Legas, Mr. Kayode Sutton, ya gabatar a ranar Lahadi a birnin Ikkon Legas.

Da ake tunawa da ranar malamai ta duniya a karshen makon da ya gabata, an gudanar da taron bayar da kyautar ne a farfajiyar taron kasa ta Eagle Square da ke birnin Abuja.

An bayar da kyautar ne duba da irin kwazon da malamai da kuma makaratun kasar ke yi a bangaren ilimi wajen bunkasa koto da karantaswa.

Kwamishinan ilimi ta jihar Legas, Mrs Folasade Adefisayo, ta ce babu shakka malaman uku sun cancanci wannan kyauta. Hakazalika ta ce zagayowar ranar Malamai ta duniya ta yi daidai da lokacin bikin karrama malaman.

KARANTA KUMA: Dole Iyaye Mata su mike tsaye domin yakar ta'ammali da miyagun kwayoyi - Dolapo Osinbajo

Ta ce kasancewar Legas jiha mai zaman kanta, tana da dama gami da kwarewar ta kai wa kololuwar mataki na samar da ingataccen ilimi ga manyan gobe. Haka kuma ta ce dole ne ta yaba wa kwazon malaman duba da jajircewarsu, sadaukar da kai da kuma kwallafa rai a kan sana'arsu.

Ta kara da cewa, babu wata al'umma da za taka mataki na ci gaba face ta zage dantsen ta wajen samar da ingataccen ilimi wanda ba ya taba tabbata sai da magartan malamai.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel