Dole Iyaye Mata su mike tsaye domin yakar ta'ammali da miyagun kwayoyi - Dolapo Osinbajo

Dole Iyaye Mata su mike tsaye domin yakar ta'ammali da miyagun kwayoyi - Dolapo Osinbajo

Mrs Dolapo Osinbajo, uwargidan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Talatar da ta gabata da gargadi iyaye mata da su yi wa kansu allurar zumbur ta mike wa tsaye domin yakar annobar ta'ammali da miyagun kwayoyi musamman a tsakanin matasa.

Ta ce annobar ta'ammali da muggan kwayoyi ta fi zama alakakai ga Mata kasancewarsu iyayen kowace al'umma, lamarin da ta ce dole su ladabtar da 'ya'yansu a kan kaurace wa dukkanin wani abun ki tare da karkatar da akalar hankulansu wajen bunkasa ci gaban kasa.

Da ta ke gabatar da jawabai kan maudu'in kawo managarcin sauyi da zai tabbatar da ci gaban kasa a taron kungiyar ci gaban Mata ta jihar Osun, OSUNWA, wadda aka gudanar a birnin Osogbo, Mrs Dolapo ta ce babu makawa ci gaban kowace kasa na da babban tasiri a kan ci gaban mata.

A rahoton da jaridar Vanguard ta ruwaito, uwargidan mataimakin shugaban kasar ta ja hankalin mata a kan tabbatar da ci gaban kawunansu ta hanyar kwato 'yanci wajen neman ilimi domin yin fito-na-fito da goga kafada da 'yan uwansu maza a kasar nan.

KARANTA KUMA: Kayayyakin da gwamnati ba ta sanya wa haraji ba a Najeriya

A yayin da ta ke jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin 'yan uwanta Mata, Dolapo ta ce kyakkyawa makomar 'ya'ya na da nasaba da irin tarbiyyar da suka samu a wurin iyayinsu Mata, lamarin da ta ce dole su tashi su kwatar wa kasar nan 'yancinta gwargwadon iko.

Kafayat Oyetole, shugaba ta kungiyar OSUNWA wadda ta kasance matar gwamnan jihar Osun, Adeboyega Oyetole, ta ce inganta hadin kai a tsakanin al'umma da kuma tabbatar da ci gaban kasa da domin talakawa su ci moriya ita ce babbar manufar da kungiyarsu ta sanya gaba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel