Kasar Italiya ta rage yawan yan majalisa daga 945 zuwa 600

Kasar Italiya ta rage yawan yan majalisa daga 945 zuwa 600

A ranar Talata, 8 ga watan Oktoba, 2019, majalisar dokokin kasar Italiya sun yi ittifakin rage yawan yan majalisan kasar domin rage tsadar mulki da yawan kudin da aka biyansu.

A yanzu, an rage yawan yan majalisa dattawa da wakilai 345 wanda yayi daidai da alkawarin da yan jam'iyyar M5S suka yiwa mutanen kasar na cewa za su yaki almubazzarancin da ake yi da kudi ga yan majalisa.

A zaben da aka gudanar jiya, mutane 553 sun amince da ragewa, mutane 14 sun ce a'a, yayinda mutane biyu suka ce basu can, basu nan.

Gabanin ragewa, Kasar Italiya ce mafi yawan yan majalisu bayan kasar Birtaniya. Suna da yan majalisar wakilai 630 da yan majalisar dattawa 315.

Yanzu an rage yawan yan majalisar wakilai zuwa 400 yayinda aka rage na majalisar dattawa zuwa 200.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da kwamitin basa shawara kan tattalin arziki

A Najeriya kuwa, yan majalisan suna cigaba da yin kunnenshi duk da cewa albashin da suke kwasa ya fi kasafin kudin da aka yiwa ma'aikatar kiwon lafiya da ilimi a hade.

Najeriya yanzu na da yan majalisan wakilai 360 da yan majalisar dattawa 109. Kowani dan majalisar wakilai na dauka akalla milyan 8 a kowani wata yayinda kowani dan majalisan dattawa na daukan milyan 14 da rabi a wata.

A makon da ya gabata, daya daga cikin yan majalisan dattawan, Rochas Okorocha, ya yi kira ga majalisar cewa Najeriya bata bukatan Sanatoci 3 da kowani jiha, ya kamata a rage zuwa sanata 1 ga jiha.

Idan akayi hakan, za'a rage yawan sanatoci daga 109 zuwa 37.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel