Gwamnan APC ya tsige hadiminsa bayan ya yi wa Mai dakinsa izgili

Gwamnan APC ya tsige hadiminsa bayan ya yi wa Mai dakinsa izgili

Kamar yadda muka samu labari a yan kwanaki da suka gabata, mun kawo maku cewa Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya tsige hadiminsa Augustine Pelemo, mai bashi shawara akan harkokin siyasa.

Kwamishinan labarai a jihar, Donald Ojogo ne ya bayyana batun tsige Pelemo a wani jawabi da ya saki a ranar Litinin da ta gabata.

Ojogo ya bayyana cewa umurnin ya zo ne dangane da bukatar samar da nutsuwa ta hanyar samar da matakan da zasu inganta zaman lumana da aminci a gwamnatin jihar.

Sai dai kuma wata majiya a ofishin mataimakin gwamna yace sallamar Pelemo da aka yi yana da dangantaka da wani rubutu da ya wallafa a shafin Facebook akan matar Agbooa Ajayi, mataimakin gwamnan jihar.

Yayin da yake mata fatan alkhairi a lokacin zagayowar ranar haihuwarta a ranar Lahadi, ya yi izgilanci ga uwargidar gwamnan, inda ya ambaci matar Ajayi a matsayin mukaddashin uwargidar gwamna.

KU KARANTA KUMA: Jerin abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da kasafin kudin 2020

"Barka da zagayowar ranar haihuwar mukaddashin uwargidar gwamnan jihar Ondo, Cif Misis Ajewole Agbola Ajayi, Allah ya kara tsawon rai," kamar yadda ya rubuta.

An tattaro cewa an sallame shi ne saboda wannan abu da ya wallafa a shafin nasa, inda aka tambayi ko yana son kawo rabuwar kai a gwamnatin ne.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Akeredelu a halin yanzu yana hutu amman matarsa ta cigaba da gudanar da ayyukanta.

Da aka bukace shi yayi tsokafi kan lamarin, Segun Ajiboye kakakin gwamnan yace: “ku bi abinda aka bayyana a jawabin.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel