An sace wani babban malamin addini a jihar Nasarawa

An sace wani babban malamin addini a jihar Nasarawa

Rundunar yan sanda reshen jihar Nasarawa ta tabbatar da sace wani limamin coci, Mista John Egla, wanda ya kasance faston cocin Christian Church of God (RCCG) a Lafia.

Kakakin Rundunar reshen, Mista Nansel Ramhan ya tabbatar da lamarin a wata hira tare da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba, 9 ga watan Oktoba, a Lafia.

Lamarin ya kasance na baya-baya daga cikin sace-sacen mutane da ake a Najeriya cikin yan kwanakin nan, duk da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi wajen ganin ta magance matsalar.

Rahman ya bayyana cewa an sace Egla ne a gidan shi dake kauyen Shabu a wajen Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa shugaban yan sanda mai kula da ofishin yan sandan dake Shabu ya sanar da rahoton jin karar harbe-harben bindiga misalin karfe 1:16 na dare.

Ya bayyana cewa a lokacin da ya kai inda lamarin ya auku, tawagar yan sanda sun gano cewa yan bindigan sun yi garkuwa da faston wanda ya kasance tare da iyalansa.

Rahman yace yan sandan sun sami harsashin AK47 a inda lamarin garkuwan ya faru da kuma cewa rundunar yan sanda ta tura jami’anta don ceto Egla.

Wani babban Faston RCCG, Mista Falaye Ominiyi wanda ya tabbatar da lamarin ya bayyana cewa fastonEgla ya kasance mai kulawa da cocin reshen Nasarawa.

KU KARANTA KUMA: An bawa malaman Islamiyya 6 masauki a gidan gyaran hali a Kaduna

Omoniyi ya bayyana cewa matar da sauran iyalan faston sun shiga cikin halin damuwa bisa afkuwar lamarin, ko da dai babu wanda ya ji rauni a lokacin harin.

Ya bukaci jami’an tsaro dasu dauki mataki don kubutar da faston.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel