Bashin Naira Biliyan 30 ta sa hukumar NERC ta na neman hana DISCOs aiki

Bashin Naira Biliyan 30 ta sa hukumar NERC ta na neman hana DISCOs aiki

Hukumar da ke lura sha’anin wutar lantarki a Najeriya ta NERC ta rubutawa kamfanoni 8 da ke da alhakin raba wuta takarda inda ta yi barazanar karbe lasisinsu a dalilin bashin da ke wuyansu.

Bashin Naira biliyan 30.1 da ake bin wadannan kamfanonin wuta ne ya sa wani Kwamishinan NERC ya nemi su yi bayani mai gamsarwa cikin kwana 60 domin su ceci lasisin aikinsu.

Dafe Akpeneye wanda ke kula da harkar lasisi da wasu al’umura na hukumar NERC ta kasa ya rubutawa kamfanonin DisCos takarda ne game da bashin da aka biyo su a karshen Watan Yuli.

NERC ta zargi kamfanonin da ke rabawa jama’a wuta a shiyyoyin Abuja, Benin, Enugu, Ikeja, Kano, Kaduna, Fatakwal, da Yola DisCos da kin biyan hukumar NBET kudin wutan da ta sha a lokacin.

Kamfanonin sun sha wutan Naira biliyan 36.1 a Watan Yulin 2019, amma abin da su ka biya hukumar NBTE Naira biliyan 5.91 ne kacal. Binciken da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna haka.

KU KARANTA: Najeriya za ta kashe Biliyan 700 wajen gina abubuwan more rayuwa

Kashi 16% na kudin wutan da aka ba DisCos ne ya fito don haka hukumar NERC ta sa baki domin ganin kamfanonin raba wutan sun biya wannan bashi da ake binsu na fiye da Naira biliyan 30.

Binciken da aka yi ya nuna cewa kamfanin DisCo na Enugu sun fi kowa laifi. A cikin kudin da ake bin kamfanin na Naira biliyan 4.112, abin da aka iya samu a watan Yulin shi ne miliyan 400.

Abuja DisCo mai alhakin biyan biliyan 7.2 na wannan bashi sun buge ne da biyan Naira biliyan 2.152. Haka kamfanin da ke raba wuta a yankin Benin ya biya miliyan 700 ne cikin biliyan 4.37.

Ana bin Kamfanin wutan na Kaduna bashin biliyan 3.427, haka zalika akwai bashin Naira biliyan 2.5, 1.76, 4.45, da kuma biliyan 3.3 a kan kamfanonin DisCo na Kano, Yola, Ikeja, da na Fatakwal.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel