Jerin malaman jami'a 6 da aka dakatad kan laifin neman lalata da dalibansu

Jerin malaman jami'a 6 da aka dakatad kan laifin neman lalata da dalibansu

Binciken da BBC Afrika ta gudanar a kwanakin nan ba shi bane lokaci na farko da ake kama malaman jami'a suna neman lalata da dalibansu mata domin taimaka musu da maki ba.

Wannan abu yana faruwa a kusan dukkan jami'o'i da kwalejin ilmi da fasaha a Najeriya.

Abune wanda ya bayyana karara cewa dalibai mata da yawa sun fuskanci irin wannan abu a jami'a.

A watan Mayu, 2016, majalisar dattawan Najeriya ta yi kokarin sanya doka shekaru biyar a gidan yari ga duk malamin da aka kama da wannan laifi amma kungiyar malaman jami'a ASUU suka dakile yunkurin.

Ga jerin Malamai 6 da aka kama kamun kugu:

1. Farfesa Richard Akindele

Ya kasance malami a tsangayar ilmin akawu a jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) kuma ya shiga hannu ne yayinda ya bukaci wata daliba mai sune Monica Osetoba Osagie ta kwanta dashi don ya kara mata maki.

Jerin malaman jami'a 6 da aka dakatad kan laifin neman lalata da dalibansu

Richard
Source: Depositphotos

2. Dr. Olabode Ajoniyi

An damke Malamin jami'ar jihar Osun din ne a wani bidiyo da ya bayyana yana lalata da wata dalibarsa mai suna Mercy Ikwue.

Jerin malaman jami'a 6 da aka dakatad kan laifin neman lalata da dalibansu

Jerin malaman jami'a 6 da aka dakatad kan laifin neman lalata da dalibansu
Source: Facebook

3. Dr Boniface Igbenuhue

Asirinsa ya tonu ne a binciken da BBC ta gudanar kwanan nan idan ya bukaci lalata da wata yarinya yar shekara 17 domin samar mata admisho jami'ar. Boniface ya kasance babban malamin cocin Foursquare kuma tuni jami'ar da cocin sun sallamesa.

Jerin malaman jami'a 6 da aka dakatad kan laifin neman lalata da dalibansu

Boniface
Source: UGC

4. Olaleye Aduwo

Wani malamin jami'ar jihar Ekiti wanda aka kama cikin wani faifan bidiyo yana kokarin lalata da wata dalibarsa don ya kara mata maki.

5. Sunkanmi Odubunmi

Jerin malaman jami'a 6 da aka dakatad kan laifin neman lalata da dalibansu

Jerin malaman jami'a 6 da aka dakatad kan laifin neman lalata da dalibansu
Source: UGC

Malami a jami'ar Legas LASU ya shiga hannu ne yayinda yake kokarin lalata wata dalibar tsangayar tattalin arziki.

Bayan bincike, an damke wasu malamai uku masu irin dabi'ar kuma an sallamesu.

6. Malami a jami'ar Abuja'

Wani malamin jami'ar Abuja da aka sakaye sunansa ya shiga hannu ne bayan an damkeshi a Otal dake unguwar Gwarimpa inda yaje lalata da daya daga cikin dalibansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel