Mun yi gagarumin nasara wajen dagargaza Boko Haram - Buhari

Mun yi gagarumin nasara wajen dagargaza Boko Haram - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace kasar tayi gagarumin nasara wajen rage karfin yan ta’addan Boko Haram.

Buhari ya yi ikirarin ne a yayin kaddamar da jami’an sojin sama na cadets 111 cikin rundunar sojin saman Najeriya (NAF) a matsayin matukan jirgin sama a sansanin NAF dake Kaduna.

Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Abayomi Olonisakin, Shugaban ma'aikatan tsaro, yace an sanya wadanda ke yunkurin tarwatsa kasar cikin mawuyacin hali.

Ya bukaci sabbin jami’an da aka kaddamar dasu fuskanci “makiyanmu” tare da yin amfani da sabbin dabaru.

Buhari yace a shekaru hudu da suka gabata, rundunar sojin sama ta gyara jiragen da suka lalace, ta kuma shigo da sabbin jirage sannan kuma cewa a hakan ne rundunar ta iya cimma “bukatun gwamnati da jin dadin da jami’anta kee bukata.”

KU KARANTA KUMA: Jerin abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da kasafin kudin 2020

A wani labarin kuma mun ji cewa rahoton SB Morgen, wata kafa bayanan sirri ta yankuna, ta ce, 'yan ta'addan dai na kara kwace wasu yankuna tare da kirkiro sabbin salon mallake yankunan arewa maso gabas din.

Rahoton ya ce, 'yan ta'addan sun rage kai farmaki ga mutane ne don su samu goyon baya tare da kara dakarunsu, amma kuma sun dage wajen harar jami'an tsaro.

Rahoton ya kara da cewa, hare-haren suna zuwa ne daga Boko Haram ta bangaren Shekau ne, wacce har yanzu take cin karenta babu babbaka a yankin kudancin Barno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel