Yadda Gwamnatin Buhari za ta kashe makudan kudi a 2020 domin kawo cigaba a Najeriya

Yadda Gwamnatin Buhari za ta kashe makudan kudi a 2020 domin kawo cigaba a Najeriya

A Ranar 8 ga Watan Oktoba 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa a gaban ‘yan majalisar tarayya inda ake sa ran kashe Tiriliyan 10.33 a badi.

A kasafin na 2020, an warewa ma’aikatar ayyuka da gidaje kaso mafi tsoka na Naira biliyan 262. Ma’aikatar wuta za ta samu Naira biliyan 123, yayin da ma’aikatar sufuri da tsaro su ke biye.

Kusan Tiriliyan biyu da rabi na kudin da za a batar a 2020 za su tafi ne waen biyan bashin da ke kan kasar. Kusan Naira biliyan 300 aka warewa shirin nan na Sukuk duk a cikin shekarar 2020.

Akwai wadanda aka ware masu kudinsu a gefe, sun hada da: Majalisa wanda za ta lashe Biliyan 125, yayin da bangaren shari’a su ka tashi da Biliyan 110. Ba a bar UBEC da NDDC a baya ba.

Sauran wadanda aka warewa kudi masu yawa sun hada da ma’aikatar harkar gona, ma’aikatar ruwa, hukumomin Arewa ta Gabas da Neja-Delta, bangaren ilmi da lafiya da kuma birnin tarayya.

KU KARANTA: Yan Majalisa sun shirya lokacin gama aiki a kan kasafin kudin 2020

Abin da ma’aikatu za su kashe a albashi ya tsaya ne a kan Naira biliyan 426.6, karin da aka yi wannan shekarar ya shafi sababbin,ma’aikatun da aka kirkira a bana ne kurum inji Buhari.

Ganin irin abin da aka kashewa kan albashi ya sa gwamnati ta bukaci ma’aikatu su rika neman izni kafin su dauki ma'aikata. Daga yanzu za a daina biyan ma’aikatan da ba su hau IPPIS ba.

Biliyan 720 da aka ware wajen ayyukan more rayuwa a shekara mai zuwa ya gaza 30% da gwamnatin tarayya ta yi wa kanta alkawari a shirin ta na babbako da tattalin arzikin Najeriya.

Buhari ya kuma bayyana cewa duk da a yanzu abin da gwamnati za ta kashe kan ayyuka ya ragu, sun samo hanyar cigaba da gina abubuwan more rayuwa ta hanyar hada-kai da ‘yan kasuwa.

Inda aka ga babban canji shi ne a ma’aikatar SIP mai taimakawa marasa galihu inda aka rage kasafinta daga Biliyan 500 zuwa Biliyan 30. Sai dai har yanzu babu canji a kudin ‘yan majalisa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel