Jerin abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da kasafin kudin 2020

Jerin abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da kasafin kudin 2020

A ranar Talata, 8 ga watan Oktoba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar na sheekarar 2020 a gaban majalisun dokokin tarayya wanda ya zarce naira tiriliyan 10.

Harma mun ji cewa Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya ce akwai bukatar Najeriya ta dawo amfani da tsarin Janairu zuwa Disamba na kasafin kudi, inda ya ce majalisa ta shirya tsaf domin yin bita tare da gabatar da kasafin da Shugaba Buhari ya kawo gabanta.

Don haka muka yi amfani da wannan fage wajen kawo maku wasu muhimman abubuwa game da kasafin kudin na 2020 wanda ya banbanta shi da na baya.

1. Akwai kyakyawar alaka tsakanin bangaen zartarwa da na dokoki a yanzu: A lokacin da shugaba Buhari ya isa zauren majalisar dokokin tarayyar don gabatar da kasafin kudin, majalisar ya dauki sowa da murna na 'Sai Baba', sabanin a lokacin gabatar da kasafin 2019, inda wasu daga cikin 'yan majalisar suka hau yi wa Shugaban Ihu a yayin gabatar da kasafin.

2. Kafin fara gabatar da jawabin daftarin kasafin na 2020, Shugaba Buhari cikin raha ya sanar da zauren majalisun cewa yana fama da mura a saboda haka a gafarce shi.

3. An kafa tarihi a kasafin kudin 2020: Wannan shine karo na farko da wani Shugaban kasa a Najeriya ke gabatar da kasafin kudi da wuri a tarihin kasar.

4. Kasafin kudin 2020 ya kafu ne a kan dala 57 farashin gangar danyen mai kuma bisa gangar danyen mai miliyan 1.86 da kasar za ta rinka fitarwa a kullum.

5. Kasafin 2020 ya kai naira tiriliyan 10.33, wanda hakan na nuni da cewa an samu karin kaso 9.7 a kan na bara.

6. A kasafin kudin bara, an ware naira tiriliyan 2.14 domin biyan basussuka, inda a kasafin 2020 aka ware naira tiriliyan 2.45 domin a biya basukan.

KU KARANTA KUMA: Kotu a jihar Kano ta damke wani Malamin jami'a da ta kama shi yana kokarin lalata da dalibar shi

7. Akan gibin da kasafin na 2020 yake da shi kuwa, Shugaba Buhari ya ce akwai gibin naira tiriliyan 2.18, inda kasafin bara yake da naira tiriliyan 1.86.

8. A kasafin na 2020, an ware naira tiriliyan 2.46 ga manyan ayyuka, inda a 2019 aka ware naira tiriliya 2.28 abin da ke nuna karin naira biliyan 18 a kan na bara.

9. Shugaba Buhari ya sanar da kara haraji a kan kayayyaki daga 5% zuwa 7.5%, domin cikasa gibin kasafin na 2020.

10. Ma’aikatar ayyuka da gidaje ce ta samu kaso mafi tsoka na naira biliyan 262 a kasafin kudin 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel