Ifeanyi Okowa ya yi na’am da shirin dawo da shinge kan hanyoyi da sharadi

Ifeanyi Okowa ya yi na’am da shirin dawo da shinge kan hanyoyi da sharadi

Gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa ya nuna cikakken goyon bayansa ga shirin da gwamnatin tarayya ta ke yi na dawo da shingen shiga Birane a kan manyan hanyoyin gwamnati.

Mai girma gwamna Ifeanyi Okowa ya nuna cewa bai da matsala da daura shinge a titunan gwamnatin tarayya muddin gwamnatin kasar ba za ta rika wuce gona da iri wajen kulawa ba.

Sanata Ifeanyi Okowa ya nemi gwamnatin tarayya ta daurawa ‘yan kasuwa wannan aiki ne a lokacin da Manema labarai su ka yi masa tambaya a kan wannan shirin da gwamnatin ta ke yi.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, ‘Yan jarida sun jefawa gwamnan jam’iyyar adawar wannan tambaya ne sa’ilin da su ka yi wata ganawa da shi a Asaba a Ranar 8 ga Oktoban 2019.

KU KARANTA: Ba duka 'Ya 'ya na na ba mukami ba, daya ce kurum ta samu - Okowa

Gwamnan yace: “Titunan mu su na rakwakkwabewa, karfin tattalin arzikinmu ya na raguwa a daidai lokacin da ake rububin arzikin kasa. Don haka ya kamata a kafa shinge ana tatsar kudi.”

“Amma bai kamata ya zama yadda aka saba yi da ba, inda gwamnati ta ke lura da harkar. A ba ‘yan waje aikin ta yadda za a rika amfani da kudin da aka tara wajen gyara hanyoyin na mu.”

“Ya fi sauki ga mutum ya biya kudi ya hau titi mai kyau a kan ya kashe kudi wajen man fetur da gyaran mota a kan mugayen tituna. Tsoron mutane shi ne wasu su sace kudin ba a yi aikin ba.”

“Gwamnatin tarayya su jagoranci aikin. Su nemi hanyar lura da lamarin, idan aka yi haka, cikin shekaru biyar, za a gyara titunanmu.” Inji Okowa wanda ya tabo batun gyara titunan tarayya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel