Tirkashi: Saura kwana daya a daura auren su, ango yaje yayi fashi a banki saboda ya samu kudin da zasu sha hidimar biki da amaryar shi

Tirkashi: Saura kwana daya a daura auren su, ango yaje yayi fashi a banki saboda ya samu kudin da zasu sha hidimar biki da amaryar shi

- Wani ango yaje yayi aikin da yazo yana yin dana sani, yayin da yaje yayi fashi a banki

- Ana saura kwana daya a daura masa aure ne dai yaje banki yayi fashi da makami

- Ya bayyana cewa yayi hakan ne saboda ya nemi kudin da zai hidimar bikin ya rasa

Saura kwana daya a daura musu aure, wani mutumi dan garin Texas dake kasar Amurka yaje yayi fashi da mamaki a banki domin ya samu kudin da zai siyawa amaryar shi zoben da za ta sanya da kuma wajen da za'a sha shagalin biki.

Shugaban rundunar 'yan sanda na yankin, Woody Wallace ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, Heath Bumpous dan shekara 36 dake zaune a yankin Crockett, kimanin kilomita 100 daga garin Houston, yaje yayi fashi da makami a Citizens State Bank a ranar Juma'ar nan da ta gaba ta 4 ga watan Oktoba.

A cewar Wallace, wanda ake zargin ya tabbatar da cewar ya aikata laifin cewa yayi fashi da makamin a bankin.

Ya ce lokacin da ya shiga bankin ya bayyana musu cewa yana dauke da makami a jikinsa, inda ya bukaci su bashi kudi. Wallace yace Bumpous ya bar bankin dauke da kudi.

KU KARANTA: Wata sabuwa: An fara yiwa 'yar jaridar BBC da ta bankado yadda Malamai ke lalata da dalibai a jami'a barazanar kisa

Amaryar da zai aura ta kadu matuka a lokacin da ta ga bidiyon da 'yan sanda suka saka a lokacin da yaje yake yin fashi a bankin.

Bayan sun yi magana, Wallace ya bayyana cewa amaryar ce ta roki angon nata akan ya kai kanshi wajen 'yan sanda domin ayi masa hukunci, inda yayi hakan kuma ya bayyana laifin da yayi.

"Ya bayyana cewa gobe za ayi daurin auren su, kuma bashi da isashen kudin da zai sayi zoben da zai bawa matarshi, bayan haka kuma yana bukatar kudin da zai kama wajen shagalin biki," in ji Wallace.

Ya kara da cewa jami'ansu sun samu nasarar karbar kudin da Bumpous ya sace kuma bikin nashi bai samu ba ranar Asabar din.

Yanzu haka dai an kai Bumpous gidan yari bayan an kama shi da laifin fashi da makami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel