Iskancin jami'a ba a kan maza ya tsaya kawai ba, Malamai mata ma suna bukatar dalibai suyi lalata da su kafin su basu maki - 'Yar jarida

Iskancin jami'a ba a kan maza ya tsaya kawai ba, Malamai mata ma suna bukatar dalibai suyi lalata da su kafin su basu maki - 'Yar jarida

Wata 'yar jarida 'yar kasar Ghana tayi magana akan binciken da BBC ta yi akan lalatar da malaman jami'a keyi da mata kafin su basu maki

Wani bincike da aka yi da yake ta faman yawo a kafafen sadarwa a jiya Litinin 7 ga watan Oktoba, ya bankado yadda malaman jami'a suke yin lalata da dalibai kafin suyi musu abinda ya kamata.

Da take mayar da martani akan wannan lamari, Gifty Anti wacce take 'yar jarida ce a kasar Ghana ta bayyana cewa abin ba a iya malamai maza ya tsaya kawai ba, wasu malamai matan ma suna yin lalata dalibai kafin su basu maki.

Matar ta wallafa wannan magana a shafinta na Instagram, inda ta ce wannan abu ya jima yana faruwa a makarantun firamare dana sakandare a kasar Ghana.

Gifty ta bayyana cewa wasu malaman makaranta a yankin Brong-Ahafo har karba-karba suke yi da dalibai mata 'yan ajin firamare na karshe kafin su basu makin da zasu shiga sakandare.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Daga taimako Mansura Isah matar Sani Danja ta shiga tsaka mai wuya (Bidiyo)

Ta bayyana cewa kasashen na cikin wani hali, dan haka muna bukatar mu tashi tsaye wajen kawo karshen irin wannan abu dake faruwa.

Idan ba a manta ba dai jiya ne dai aka dinga maganganu a kafafen sadarwa kan yadda malamai ke yin lalata da dalibai kafin su basu maki, inda har aka dakatar da wani malami a wata jami'a a jihar Legas bayan an kama shi da laifin lalata da wata daliba da take neman gurbin karatu a makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel