Kundin kasafin kudin 2020 zai bar hannun Majalisa a Ranar Nuwamba 28 - NASS

Kundin kasafin kudin 2020 zai bar hannun Majalisa a Ranar Nuwamba 28 - NASS

Majalisar Tarayyar Najeriya ta fadi lokacin da ta ke sa rai za ta kammala aikinta a kan kasafin kudin kasar na shekara mai zuwa. Majalisar ta bayyana wannan ne a ranar da ta karbi kundin.

Kamar yadda mu ka samu labari daga bakin shugaban kwamitin yada labarai na majalisar wakilan tarayyar, kundin kasafin kudin zai bar hannun majalisa ne a Ranar 28 na Nuwamba.

Honarabul Benjamin Kalu ya bayyana wannan a jiya Talata 8 ga Watan Oktoban 2019 lokacin da yake zantawa da Manema labarai. Kalu shi ne mai magana a madadin ‘Yan majalisar wakilai.

Benjamin Kalu yace su na da sha’awar ganin tsarin kasafin kudin ya koma aiki daga Watan Junairu zuwa Disamba. Kalu yace za a iya cin ma wannan buri domin an kafa kwamitoci.

“Mun shirya ganin an sauya tsarin kasafin kudi daga yadda ake a kai yanzu a komawa tsarin Junairu zuwa Disamban duk shekara. An ci sa’a an rantsar da duk wani kwamiti a majalisa.”

KU KARANTA: Ba za mu bata lokaci wajen aikin kasafin kudi ba - Lawan

Ya ce: “Domin a maida hankali kan aikin kasafin kudi, Majalisa za ta dakatar da duk wani zama – ba wai majalisa za ta daina aiki ba. – Wannan zai ba mu damar zaman kwamiti da MDAs.”

A bayanin da Hon. Kalu ya yi wa ‘yan jarida, ya bayyana cewa majalisa za ta gana da shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya domin ganin an gama aikin kasafin kudin kasar.

Kalu yace a Ranar 30 ga Oktoba majalisa za ta yi zama da hukumomin gwamnati kan kudin da aka warewa sha’anin tsaro ta. Za kuma a saurari jama’a a Ranar Oktoba 21 da 22 a majalisar.

Bayan 5 ga Watan Nuwamba, ‘dan majalisar kasar yace ba za su sake karbar wani rahoto daga wata ma’aikata ba yayin da daga 6 ga Watan Nuwamba, za a fara shirin kakkabe wannan aikin.

“Zuwa Nuwamba 28 kwamitocin majalisar wakilai da dattawa za su yi zaman karshe. Abin da mu ke so shi ne daga farkon Dismba an gama da kundin, sai ya fara aiki a farkon 2020.” Inji Kalu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel