Gombe: Yadda wani matashi ya caka wa abokinsa wuka a kirji saboda abinci

Gombe: Yadda wani matashi ya caka wa abokinsa wuka a kirji saboda abinci

'Yan sanda sun kama wani Abubakar Abdullahi dan shekara 17 mazaunin Idi Quarters a Gombe da aka ce ya dabawa wani Yusuf Suleiman dan shakra 15 wuka yayin rikici da ya barke tsakaninsu saboda rabon masa.

The Punch ta ruwaito an gano wata sharbebiyar wuka a hannun wanda ake zargin da ake kyautata zaton da ita ya yi amfani wurin kashe wanda abin ya faru da shi.

Wannan bayanin na cikin wata sanarwa da Kakakin 'yan sandan jihar, SP Mary Malum ta aike wa Northern City News da ke Gombe a ranar Talata.

Malum ta ce 'yan sanda masu aiki a sashin kisar gilla ne jihar Gombe ne suka kama wanda ake zargin.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP tayi babban rashin wani jigon ta

Ta ce, "Abdullahi ya caka wa wani Yusuf Suleiman wuka a kirjinsa sakamakon rashin jituwa da ya shiga tsakaninsu wurin rabon abinci (masa). An gano wata doguwar wuka daga hannun wanda ake zargin; Ana cigaba da bincike kan lamarin kuma daga bisani za a gurfanar da shi a kotu."

Kazalika, 'Yan sandan Gona sun kama wani Wada Saleh, dan shekaru 19 mazaunin Hayin Dogo Nasarawa Quarters kan zargin fyade.

Ana zargin cewa ya shigar da wata 'yar shekaru 8 cikin daji kuma ya sadu da ita.

Wani sashi na rahoton ya ce, "Saleh ya sake maimaita abinda ya aikata amma a wannan karon cikin wani kango ya kai ta kafin asirinsa ya tonu aka kama shi.

"An garzaya da yarinyar zuwa asibitin kwararru na Gombe domin ba ta kulawa."

Mai magana da yawun 'yan sanda ta ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma za a gurfanar da shi a kotu ta zarar an gama bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel