Assha: An sallami shugaban ASUP da sakatarensa

Assha: An sallami shugaban ASUP da sakatarensa

Mahukunta a Kwalejin Fasaha ta Rufus Giwa da ke Owo a ranar Talata sun kori Mista Oluwadare Ijawoye, shugaban kungiyar malamai na kwallejin Fasaha (ASUP) da kuma sakatarensa, Ade Arikawe a kan almubazaranci da kudi.

Kamafanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa ASUP ta zargi wasu manyan jami'an makarantar da shugaban majalisar mahukunta na makarantar da almubuzaranci da kudade a bayan lokacin da suka siyo wasu motocci.

Takardar sallamar na cikin wani sako ne da mahukunta makarantar suka aike wa NAN a Akure ta hannun Samuel Ojo, Direktan sashi hulda da al'umma na makarantar kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP tayi babban rashin wani jigon ta

Sanarwar tayi gargadin cewa ba a bukatar ganin wadanda aka kora din a harabar makarantar kuma al'umma su sani cewa makarantar ba za ta sake wani wani harka da su ba.

Kazalika, sanarwar ta kuma ce an dakatar da ayyukan kungiyar ASUP a makarantar.

Sanarwar ta ce, "Daga yanzu an kori mutanen biyu a matsayin shugaba da sakataren ASUP.

"Duk wanda ya yi wata harka tare da su yana yin gaban kansa ne kuma ya kuka da kansa idan ya ga ba dai-dai ba."

Korar shugaban na ASUP da sakatarensa na zuwa ne bayan bata kashi da aka dade ana yi tsakanin kungiyar da mahukunta kwalejin.

Mr Ijawoye ya zargi mahukunta jami'ar da ware kudi naira miliyan 68 domin sayo a kalla motoci biyar da ya yi ikirarin cewa dukkansu ha hannu ne.

Ya ce abinda suka aikata ya saba wa doka a jihar Ondo.

Mista Ijawoye ya ce tuni kungiyar ta shigar da kara wurin hukumar yaki da rashawa inda ya ce a nan gaba za su fitar da cikaken bayani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel