Amotekun: Gwamnonin Kudu maso Yamma sun kafa Runduna domin ba Jami’an tsaro gudumuwa

Amotekun: Gwamnonin Kudu maso Yamma sun kafa Runduna domin ba Jami’an tsaro gudumuwa

Labari ya zo mana daga Jaridar The Cable a Ranar 8 ga Watan Oktoban 2019 cewa Gwamnonin jihohin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya za su yi hobbasa game da sha’anin tsaron yankin.

Gwamnnonin za su hada kai ne su ba manyan jami’an tsaro motoci 100 da za su rika amfani da su wajen sintiri domin yakar rashin tsaro a yankin. Gwamnonin kuma za su saye wasu kayan aikin.

Wadannan gwamnoni na kasar Yarbawa sun kafa wani tsarin tsaro na mai suna “Amotekun” inda za su hada karfi da karfe da juna domin samar da isassun kayan sadarwa da sufurin jami’an tsaro.

Gwamnonin shidda su ne Ondo, Ogun, Osun, Ekiti, sai kuma jihohin Legas da Oyo. Gwamnan jihar Ogun, Mai girma Dapo Abiodun, ya bayyana wannan a Ranar Litinin 7 ga Watan Oktoban 2019.

A jawabin gwamnan, ya ce kowanensu zai bada motoci 20 da kuma kayan aiki tare da daukar nauyin Dakarun da za su yi wannan aiki domin inganta tsaro a jihohin na Kudu maso Yamma.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe wasu Bayin Allah ana zaune kalau a Filato

A Watan Yuli ne gwamnonin Yankin na kasar Yarbawa su ka taru su ka amince su ka kafa wata babbar runduna da za ta yaki matsalar rashin tsaro gadan inda su ka samu amincewar gwamnati.

Gwamnonin sun samu damar kafa wannan runduna daga ofishin NSA watau mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro. Wannan ya na cikin manufofin hukukmar gwamnonin shiyyar.

“Abin kunya ne ace jami’an tsaro ba su da na’urorin sadarwa, ma’ana Kwamishinan ‘yan sanda ba zai iya magana kai-tsaye da Sojojo ko DSS ba, kai ba zai ma iya magana da DPO dinsa ba.”

“Motocinsu ba su aiki, babu na’urori, babu kudi, saboda haka mu ke kokarin gyara wannan matsaloli da gidauniyar da mu ka kafa na tsaro.” Inji Gwamnan wajen taron kafa gidauniyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel