Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: ‘Yan bindiga sun kashe jama’a da dama tare da satar shanu a wani kauyen Sakkwato

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: ‘Yan bindiga sun kashe jama’a da dama tare da satar shanu a wani kauyen Sakkwato

Wadansu mutanen da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai harin kauyukan Tarana da Mahuta dake karamar hukumar Tureta a jihar Sakkwato inda suka kashe mutane da dama tare da yin satar shanu.

A cewar wata majiya daga kauyen da wannan abu ya faru, ta sanar damu cewa ‘yan bindiga sama da mutum 100 ne suka dira kauyukan biyu da misalin karfe 7 na maraicen ranar Litinin, inda suka shiga baza wuta ga duk mutumin da suka yi arba da shi.

KU KARANTA:‘Yan bindiga sun kashe mata 3 a Barikin Ladin jihar Filato

Har ila wani daya daga cikin mazauna kauyen da wannan abin ya faru wanda ya nemi a boye sunansa, ya ce, “Bamu san hakikanin adadin mutanen da ‘yan bindigan suka kashe ba saboda mun gudu ne domin tsirar da rayuwarmu.”

Da take tabbatar mana da aukuwar wannan lamarin, rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta bamu tabbacin cewa kimanin mutane 150 wadanda ake sa ran ‘yan bindiga ne, suka dira kauyukan Tarana da Mahuta na karamar hukumar Tureta, inda suka kashe jama’a da kuma yin satar shanu da ba san adadinsu ba.

Jami’in hulda jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Abubakar Sadiq ya bamu labarin cewa: “ ‘Yan bindigan sun isa kauyukan ne ranar Litinin 7 ga watan Oktoba, 2019 da misalin karfe 7 na maraice.

“Dauke suke da muggan makamai kuma kai tsaye suka soma harbin duk wanda suka yi arba da shi, domin su firgita ‘yan kauyen inda daga bisani suka yi masu fashi.”

Duk da cewa Sadiq bai iya fadin adadin mutanen da aka kashe ba, sai dai ya bamu tabbacin cewa jami’ansu na kan gudanar da bincike a kauyukan da abin ya faru.

http://leadership.ng/2019/10/09/bandits-kill-villagers-rustle-cows-in-sokoto/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel