Jam'iyyar PDP tayi babban rashin wani jigon ta

Jam'iyyar PDP tayi babban rashin wani jigon ta

Shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Osun na farko, Chif Layi Ogunrinade ya rasu yana da shekaru 80 a duniya.

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon sakataren gwamnan jihar Osun kuma tsohon shugaban jam'iyyar na jihar Osun, Alhaji Fatai Akinade Akinbade ne ya tabbatar da rasuwar jigon jam'iyyar.

Akinbade ya bukaci jam'iyyar ta PDP reshen jihar Osun tayi wani abu da zai saka ba za a manta da Ogunrinade ba a matsayin hanyar nuna godiya bisa irin gudunmuwar da ya bawa jam'iyyar a jihar.

DUBA WANNAN: Pantami da shugaban NITDA sun kirkiri wata muhimmiyar na'ura

Akinbade ya yi wa jam'iyyar jaje da kuma iyalan marigayin cikin sanarwar da ya fitar da bakin mai magana da yawunsa, Mista Kayode Oladeji a garin Osogbo.

Ya ce, "Gudunmuwar da Ogunrinade ya bayar a siyasa ba ta gushe ba har rasuwarsa. Rasuwarsa ya bar wani gibi da zai yi wahalar samun wanda zai cike shi. Daya daga cikin hanyoyin da za a rika tunawa da shi shine saka sunansa a wani abu. Ya cancanci hakan."

Akinbade ya shawarci sauran 'yan jam'iyyar suyi koyi da irin kyawawan halayen Ogunrinade a matsayinsa na cikakken dan siyasa da dattijo da kuma shugaban al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel