Rufe kan iyaka: Duk da samun N5bn a ko wace rana, jami’an kwastam sun koka akan rashin samun alawus

Rufe kan iyaka: Duk da samun N5bn a ko wace rana, jami’an kwastam sun koka akan rashin samun alawus

Wasu daga cikin jami’an hukumar hana fasa kwauri ta kwastam sun koka a kan rashin biyansu alawus din da aka masu alkawari sakamakon aikin da suke yi a kan iyaka.

Wannan korafin na zuwa bayan ikirarin da shuagaban hukumar yayi, Hameed Ali na cewa tun bayan da aka rufe kan iyakar Najeriya a ko wace rana hukumar na samun naira biliyan 5.

KU KARANTA:Dokar hana sa hijabi: Majalisar Koli ta lamuran addinin musulunci ta bayyana fushinta a kan Jami’ar Ibadan

Jaridar Punch tattaro mana bayanin cewa hukumar ta biya jami’anta aluwas dinsu na musamman a watan Agusta daidai da mukamin ko wannensu.

Mun samu labarin cewa masu mukamin ASC an biyasu naira 380,000 yayin da wadanda ke kasa da su a mukami a biyasu kusan rabin wannan kudin.

Haka zalika, a watan Satumba kuwa sai labarin ya canja inda aka rage kudin da 80%, wanda haka ya janyo kace-nace tsakanin jami’an.

Wani jami’in hukumar wanda ya nemi a boye sunansa ya ce mana: “An sanar damu cewa a watan Agusta za a rufe dukkanin kan iyakokin kasa na shigowa Najeriya, a don haka ana bukatar muyi aiki sosai amma dai za a biyamu alawus na musamman.

“Alawus zai kunshi kudin abinci, zirga-zirga da dai da sauransu. Anyi wannan tsarin ne domin a kawar da idanunmu daga kan masu kokarin bamu cin-hanci. A matsayina na ASC an biyani naira 380,000 inda ‘yan kasa da mukamina kuwa aka biya su kimanin naira 200,000.

“Tanadin da aka yi nafarko shi ne a rufe kan iyakokin na wata guda kacal. Ba tare da sanin dalili ba aka cigaba da rufe kan iyakokin, yanzu haka an rage mana alawus na watan day a wuce N70,000 kawai aka bani.” Inji jami’in.

https://punchng.com/border-closure-despite-generating-n5bn-daily-customs-owes-allowances/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel