Yawan haihuwa na haifar da sankarar mahaifa – Zainab Bagudu

Yawan haihuwa na haifar da sankarar mahaifa – Zainab Bagudu

Uwargidar gwamnan jihar Kebbi, Dr Zainab Atiku Bagudu ta bayyana cewa masana sun ce cutar sankarar mahaifa ta fi tsananta ne a yankin arewacin Najeriya sakamakonyawan haihuwa da mata ke yi.

Duk da rashin isassun cibiyoyin kula da masu cutar daji a kasar, wasu bincike sun nuna cewa adadin masu kamuwa da wannan cuta na karuwa ne duk shekara a kasar, inda hakan ya zamo barazana musamman ga mata.

Shafin BBC ta ruwaito cewa Zainab Bagudu, wacce ta kasance shugaban gidauniyar MedicAid da ke bincike da kiɗayar masu fama da cutar a Najeriya da kuma bayar da tallafi, ta shaida mata cewa sankarar mahaifa ta fi shafar matan arewa, inda sankarar mama kuma ta fi shafar matan kudancin kasar.

Zainab ta ce bincikensu ya nuna sama da mutum dubu ɗari biyu da hamsim ke kamuwa da cutar kansa a Najeriya duk shekara.

KU KARANTA KUMA: An sa ranar cigaba da sauraron shari'ar Maryam Sanda da Bilyaminu Bello

Ta yi kira ga mata a arewacin ƙasar su rungumi tsarin taƙaita haihuwa a matsayin rigakafi.

Kansa dai cuta ce da ke da wuyar sha'ani da kuma tsadar magani, kuma Dr Zainab ta ce rudanin da ke tattare da cutar kansa ne ya ja hankalinta ga kafa gidauniyar yaki da cutar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel