Malamin da ake zargi da yin lalata da dalibansa Kano ya amsa laifinsa

Malamin da ake zargi da yin lalata da dalibansa Kano ya amsa laifinsa

Wani alkalin kotun Majistare a Kano a ranar Talata ta bayar da umurnin tsare wani lakcara mai shekaru 36, Ali Shehu a gidan yari saboda cin amana da keta hakkin dalibarsa.

Mista Shehu malami na a Makarantar Fasaha ta Jihar Kano wato Kano State School of Technology kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

An gurfanar da shi ne kan laifuka biyu da suka hada da cin amana da yunkurin aikata laifi wadda hakan ya sabawa sashi na 95 da 98 na dokar Penal Code.

Alkalin kotun, Mohammed Idris ya bayar da umurnin a cigaba da rike wanda ake tuhumar kuma ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 15 ga watan Oktoba domin yanke hukunci.

DUBA WANNAN: Pantami da shugaban NITDA sun kirkiri wata muhimmiyar na'ura

Da farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Badamasi Gawuna ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Augusta a Kano.

Ya ce an gano hakan ne bayan wani sumame da hukumar sauraron karrakin al'umma da yaki da rashawa na jihar Kano tayi.

Mista Gawuna ya ce a ranar da abin ya faru misalin karfe 11 na safe wanda ake zargin wanda malami ne a Makarantar Fasaha ta Kano ya dauki wata dalibarsa (da aka boye sunanta) zuwa Ummi Plaza a Kano domin taya shi makin din takardun jarrabawa.

Mai shigar da karar ya ce a yayin hakan ne, "wanda ake zargin ya amsa cewa ya taba al'aurar wace abin ya faru da ita."

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel