Kasafin kudin shekarar 2020 yunkuri ne na talauta Najeeriya, in ji PDP

Kasafin kudin shekarar 2020 yunkuri ne na talauta Najeeriya, in ji PDP

- Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta hori majalisar dattawa da ta canza akalar kasafin kudi na shekarar 2020

- Ta kara da cewa wannan kasafin kudin bai wakilci ra'ayin talakawa ba

- Jam'iyyar tace kasafin a dunkule yake kuma zai taimaka wajen kara talauta Najeriya

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta hori majalisar dattawa da ta canza akalar kasafin kudi na shekarar 2020 zuwa bangarorin da zasu zamo manyan bukatun 'yan Najeriya.

Jam'iyyar ta bada shawarar ne a takardar da sakataren yada labarai na jam'iyyar, Kola Ologbondiyan ya bada a ranar Talata a Abuja.

Shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar Talata ya mika kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dattawa wanda ya kai naira tiriliyan 10.7.

KU KARANTA: Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kara gurfanar da sirikin Atiku Abubakar

Ologbondiyan ya ce, kasafin kudin zai talauta 'yan Najeriya ne tare da sanya kasar ta kara fadawa cikin bashi a nan gaba kadan.

"Dukkanin kasafin kudin ya kasance a dunkule, cike da yaudara da kuma abubuwan da bazasu fassaru ba," in ji shi.

Hakan kuwa kamar yadda yace, zasu bada damar waskar da kudaden jama'a.

"Kasafin kudin an yi shi ne don ra'ayin wasu mutane kadan. Babu aiyukan da talakawa zasu mora," in ji shi.

Ologbondiyan ya kara da kalubalantar kasafin kudin da abinda ya zarga da "dunkulallun aiyuka", ballantana a ma'aikatar aiyuka da gidaje tare da sufuri, inda kamar yadda yace ana zarginsu da waskar da kudaden kasafin shekarar da ya gabata.

Ya kara da cewa, "A wakiltar ra'ayin miliyoyin matasa da matan Najeriya, jam'iyyarmu bata aminta da kasafin kudin nan ba. Naira biliyan 48 ta bangaren ilimi da naira miliyan 46 a bangaren lafiya bai wadatar ba. Akwai bukatar majalisar dattawa ta kara dubawa don kare ra'ayin 'yan Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel