Allura na shirin tono garma: IGP ya umurci jami’an yan sanda da su kaddamar da kadarorinsu

Allura na shirin tono garma: IGP ya umurci jami’an yan sanda da su kaddamar da kadarorinsu

Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba, ya umurci dukkanin jami’an rundunar yan sandan Najeriya da su kaddamar da kadarorinsu.

Adamu ya tunatar da jami’an yan sandan cewa wajibi ne ga jami’an gwamnati su kaddamar da dukiyoyinsu.

Adamu ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin Shugaban CCB, Farfesa Mohammed Isah, da mambobin hukumar a ofishinsa da ke Abuja.

Ya jaddada jajircewar yan sanda na taimakawa hukumar da jami’ai domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, inda ya kaa da cewar hadewar hukumomin biyu na da matukar muhimmanci domin su aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata.

A jawabinsa, Shugaban CCB Mohammed Isah, ya roki Shugaban yan sandan da ya taimaka masu, cewa hukumar ba za ta iya aiwatar da umurnin kotu ita daya ba.

KU KARANTA KUMA: Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kara gurfanar da sirikin Atiku Abubakar

Ya kara da cewa hukumar za ta nemi yan sanda domin su aiwatar da umurnin hukumar akan duk wani jami’in gwamnati yayinda ya yaba ma Shugaban yan sandan akan kaddamar da nasa dukiyoyin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel