Dokar hana sa hijabi: Majalisar Koli ta lamuran addinin musulunci ta bayyana fushinta a kan Jami’ar Ibadan

Dokar hana sa hijabi: Majalisar Koli ta lamuran addinin musulunci ta bayyana fushinta a kan Jami’ar Ibadan

Majalisar koli wadda ke lura da lamuran addinin musulunci a Najeriya wato NSCIA ta tuhumi hukumar gudanarwar Jami’ar Ibadan da yin karan tsaye ga dokar addinin musulunci yayi sanya wadansu dokoki a cikin jami’ar.

Wannan bayanin na kunshe ne cikin wani zancen da kakakin majalisar ya fitar, Aselemi Ibrahim bayan majalisar ta kammala zama na musamman a Abuja.

KU KARANTA:Majalisa ba za ta bata lokaci ba wurin tantance kasafin kudin 2020 – Lawan

Zaman wanda shi ne irinsa na bakwai ya samu halartar Shugaban majalisar kuma Sarkin Musulmin na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III.

Majalisar ta yi Allah wadan irin matsalolin rashin tsaron da ake fama da su a kasar nan, inda ta yi kira ga hukumomin tsaro da su kara zage dantse wurin samar da zaman lafiya a kasar nan.

Haka zalika, majalisar ta gargadi al’ummar musulmi da su guji yada labaran karya da duk wata jita-jita, inda ta ce su kwantar da hankalinsu game da labarin da ke yawo cewa an rushe masallaci a jihar Ribas, har yanzu kwamitin bincike bai kammala aikinsa ba, a cewar majalisar.

Majalisar tayi magana mai tsawo game da dokar hana sanya hijabi a Jami’ar Ibadan, inda ta bayyana rashin jin dadinta game da wannan doka da hukumar gudanarwar jami’ar ta sanya.

A cikin zance da majalisar kolin lamuran addinin musulunci ta fadi cewa, hukumar gudanarwar jami’an da ma makarantar sakandaren jami’ar, banda hana sanya hijabi ta na saka wadansu ababe na makarantar na cin karo da lokacin sallar juma’a.

A karshe majalisar kolin ta yi kira ga Majalisar dokokin Najeriya da ta fitar da wata doka wadda za ta halatta sanya hijabi a makarantun Najeriya baki daya.

https://www.dailytrust.com.ng/hijab-nscia-tackles-u-i-management.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel