Babu wani aibu don na bawa diya ta mukami a gwamnatina - Gwamnan PDP

Babu wani aibu don na bawa diya ta mukami a gwamnatina - Gwamnan PDP

- Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce daya kawai daga cikin 'ya'yansa mata ya bawa mukami a gwamnatinsa ba biyu

- Okowa ya ce ya bawa diyarsa mukamin ne saboda ta cancanta kuma ya san irin nagartar da diyar tasa keda ita

- Kazalika, ya bayyana cewa babu wani aibu don ya bawa diyarsa mukami, a saboda ba zai nemi afuwar kowa ba

A ranar Talata ne gwamnan jihar Delta, Dakta Ifeanyi Okowa ya ce Allah kadai keda zabin waye zai gaji kujerarsa ta gwamna a shekarar 2023.

Da yake magana yayin wata hira ta musamman da 'yan jarida a Asaba, gwamna Okowa ya ce jam'iyyar PDP zata cigaba da aiki tukuru domin tabbatar da cewa ta zama madaurinki daya tare da yin aiki da dukkan mambobinta a jihar.

DUBA WANNAN: Manyan ma'aikatu 10 da Buhari ya ware wa makudan biliyoyi a kasafin 2020

Kazalika, gwamnan ya yi watsi da labarin da ake yada wa a kan cewa ya bawa 'ya'yansa mata guda biyu mukamai a gwamnatinsa. Okowa ya ce daya daga cikin 'ya'yan ya bawa mukami, ba dukkansu ba.

"Ba gaskiya bane zancen da ake yada wa a kan bawa 'ya'yana mata guda biyu mukami. Guda daya kawai a cikinsu na nada saboda ta cancanta. Ba ni da wata diya a dandalin sada zumunta. Na bata mukami ne a bangaren ilimin 'ya'ya mata bisa cancanta. Ba na nadamar bata mukamin saboda nasan irin nagartar da diya ta keda ita," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel