Majalisa ba za ta bata lokaci ba wurin tantance kasafin kudin 2020 – Lawan

Majalisa ba za ta bata lokaci ba wurin tantance kasafin kudin 2020 – Lawan

-Sanata Lawan Ahmad ya fadi yadda Majalisa za ta yi bitar kasafin kudin 2020

-Shugaban majalisar dattawan yayi kira ga hukumomi da ma'aikatun gwamnati da cewa su halarci majalisr domin amsa tambayoyi game da kasafin kudin

-Akwai bukatar Najeriya ta dawo bisa tsarin Janairu-Disemba na kasafin kudi, a cewar Lawan Ahmad

Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya ce akwai bukatar Najeriya ta dawo amfani da tsarin Janairu zuwa Disemba na kasafin kudi, inda ya ce majalisa ta shirya tsaf domin yin bita tare da gabatar da kasafin da Shugaba Buhari ya kawo gabanta.

Lawan a cikin jawabinsa na bude taron gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa, yayi kira ga hukumomi da ma’aikatun gwamnati da su bayyana a gaban majalisar kamar yadda doka ta tanadar domin mika amincewa da kasafin da wuri.

KU KARANTA:Matashi dan shekara 21 ya bayyana a gaban kotu bayan an kama shi da bindiga

Bugu da kari, Shugaban majalisar dattawan ya fadi yadda bitar kasafin kudin zai kasance, inda ya ce, a cikin watan Oktoba za a saurari bayanai daga hukumomi da ma’aikatun gwamnati sai kuma sauran abubuwan da suka rage za a yi su cikin watan Nuwamba inda kuma ake sa ran kammala komai a watan Disemba.

A wani labari kuwa za ku ji cewa, Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi ya ce yawan ‘yan Najeriya matsala yake haifarwa bangaren cigaban kasar.

Lamido, yayi wannan maganar ne a Abuja wurin wani taro karo na 25 a kan tattalin arzikin Najeriya. Taron ya samu halartar Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da kuma babban malamin addinin kiristan nan Bishop Mathew Kukah.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel