Buhari ya yi umurnin dakatar da albashin ma’aikatan da basa cikin dandamalin IPPIS

Buhari ya yi umurnin dakatar da albashin ma’aikatan da basa cikin dandamalin IPPIS

Ma’aikatan da ba a riga an dauki bayanansu ba a cikin dandamalin gwamnatin tarayya na biyan ma’aikata na IPPIS na gab da rasa albashinsu daga karshen watan Oktoba 2019.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayyana hakan a lokacin gabatar da kasafin kudin 2020 a majalisar dokokin tarayya a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa an bayar da wani umurni na dakatar da albashin kowani gwamnatin tarayya a kokarin lura da yawan kudaden da ake kashewa jami’ai.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar kasafin kudin 2020 ga majalisar dokokin tarayya domin su duba kuma su tabbatar da shi domin aiwatarwa.

A wannan karon, Buhari ya hada da wani doka na karin kudin harajin kayayyaki. A cewarsa, wannan sabuwar doka na haraji za ta kara kudin harajin kayayyai daga 5% zuwa 7.5%.

KU KARANTA KUMA: Kiyasin da aka gina kasafin kudin 2020 a kai da hotunan taron

Amma ya bayyana cewa akwai wasu kayayyakin masarufi 21 da ya togaciye kuma wannan haraji ba zai shafesu ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel