Ainahin abunda ya sa za mu kara haraji kan kaya - Buhari

Ainahin abunda ya sa za mu kara haraji kan kaya - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa gwamnatinsa ke shirin kara haraji akana kayyakai.

A cewar Shugaban kasar, gwamnatinsa za ta gina kasafin ne a kan kudin harajin kaya na VAT saboda hakan ne zai kara yawan haraji daga kaso hudu zuwa 7.7.

Ya kara da cewa hakan ne zai bai wa gwamnatin tarayya damar cike gibin fiye da naira tiriliyan biyu da ke kasafin kudin kasar da aka gabatar yau Talata, 8 ga watan Oktoba.

Buhari wanda ya gabatar da kasafin kudin a gaban zauren majalisar dokokin kasar, ya ce kasafin na 2020 ya dara na 2019 da kaso 9.7 cikin dari.

Kasafin na 2019 dai ya kai naira tiriliyan 8.83, inda na 2020 zai kama fiye da naira tiriliyan 10.

An kafa kasafin na 2020 ne a kan farashin gangar danyen mai dala 57, inda kuma ake hasashen Najeriyar za ta rinka fitar da gangar man 1.86 a kullum.

KU KARANTA KUMA: A gaggauta daukar mataki kan keta haddin dalibai da malamai ke yi a jami'o'i - Aisha Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyanawa 'yan majalisar dattawa da wakilai cewa su yi hakuri da muryarsa a jawabin da zai gabatar saboda yana fama da mura sakamakon namijin kokarin da ya yi wajen ganin cewa ya kammala shirya kasafin kudin 2020.

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya fara gabatar da jawabinsa gaban yan majalisan inda yake bayyana kasafin kudin 2020.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel