Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kara gurfanar da sirikin Atiku Abubakar

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kara gurfanar da sirikin Atiku Abubakar

- A ranar Talata ne hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kara gurfanar da sirikin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar

- Hukumar na zarginsa da almundahanar kudi har dala dubu dari da arba'in

- Ana zargin Babalele da tirsasa wani Mohammed wajen fitar masa da makuden kudaden ne ba tare da bi ta hannun wata masana'antar kudi ba

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kara gurfananar da Abdullahi Babalele a ranar Talata akqn almundahanar kudade.

An ce Abdullahi sirikin tsohon mataimakin shugaban kasa ne, Alhaji Atiku Abubakar.

Hukumar EFCC tana zargin Babalele ne da almundahanar $140,000 a zaben shugabancin kasa da ya gabata.

KU KARANTA: Kukah ya bayyana dalilin da yasa ake yiwa sarki Sanusi II bita da kulli

An fara gurfanar da wanda ake karar ne a ranar 14 ga watan Agusta lokacin hutun kotun a gaban mai shari'a Nicholas Oweibo.

Ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi kuma an bada belinsa akan naira miliyan ashirin bayan da ya cika sharuddan belin.

Amma kuma bayan an mika shari'ar ga sabon alkali, Jastis Cjukwujekwu Aneke, sai aka kara gurfanar da wanda ake zargin a ranar Talata.

Ya kara musanta abinda ake zarginsa da shi.

Amma kuma, bayan sake gurfanar da shi da aka yi, Babalele ya bukaci kotun da ta bashi fasfotinsa na fita kasashen ketare don ya je binciken lafiyarsa.

Amma kuma lauyan masu kara, Rotimi Oyedepo wanda ya bayyana tare da A. O Mohammed, ya kalubalanci bukatar inda yace babu shaidar da ke nuna cewa ba zai iya samun maganin ciwonsa a Najeriya ba.

Jastis Aneke ya dage sauraron karar zuwa 11 ga watan Oktoba don yanke hukunci akan bukatar belin.

A tuhumarsa da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ke yi, ta zargi wanda aka gurfanar din da "Tirsasa wani Mohammed don fitar masa da kudi har $140,000 ba tare da bi ta wata masana'antar kudi ba."

Wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 20 ga watan Fabrairu.

Laifin yace karo da sashi na 162, sakin layi na 2 da kuma sashi na 18 na dokokin hani da almundahanar kudade na 2011.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel