Manyan ma'aikatu 10 da Buhari ya ware wa makudan biliyoyi a kasafin 2020

Manyan ma'aikatu 10 da Buhari ya ware wa makudan biliyoyi a kasafin 2020

A ranar Talata, 08 ga watan Satumba, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a gaban majalisar tarayya (majalisar wakilai da ta dattijai).

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyanawa 'yan majalisar dattawa da wakilai cewa su yi hakuri da muryarsa a jawabin da zai gabatar saboda yana fama da mura sakamakon namijin kokarin da ya yi wajen ganin cewa ya kammala shirya kasafin kudin 2020.

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya fara gabatar da jawabinsa gaban yan majalisan inda yake bayyana kasafin kudin 2020.

Ga jerin manyan ma'aikatu 10 da shugaba Buhari ya fi ware wa kaso mafi tsoka a cikin kasafin kudin fda ya gabatar;

1. Ma'aikatar ilimi: N48bn

2. Lantarki: N127bn

3. Noma da raya karkara: N83bn

4. Aiyuka da Gidaje: N262b

5. Sufuri: N123bn

6. Hukumar ilimin bai daya (UBE): 112bn

7. Tsaro: N100bn

8. Aiyukan agajin gagga wa: N100bn

9. Albarkatun Ruwa: N82bn

10. Yankin Niger Delta: 81bn

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel