Yan sanda sun gurfanar da magidanci akan cin zarafin matarsa

Yan sanda sun gurfanar da magidanci akan cin zarafin matarsa

Rundunan yan sanda a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba, ta gurfanar da wani mai shago mai suna, Taiwo Adekeye, dan shekara 43 bisa zargin cin zarafin matarsa.

Sai dai kuma Adekeye, wanda ya kasance mazaunin Agege a jihar Legas ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa akai.

Dan sanda mai kara, Insp. Emmanuel Ajayi yace wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 29 ga watan Disamba, a Mushin, Legas.

Yayi zargin cewa mai laifin yayi ma matarsa Toyin duka, wanda hakan ya saba ma dokar cin zarafi na jihar Legas, 2017.

Laifin yace ya saba ma sashi na 127 na dokar masu laifi na jihar Legas, 2015.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta rahoto cewa sashin tana dauke da hukuncin zaman kurkuku na shekara daya ga duk wanda ya ci zarafi.

Mai shari'a O.O. Fagbohun ya amince da bayar da belin naira N100,000 ga mai laifin tare da wanda zai tsaya masa mutum daya.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Daga taimako Mansura Isah matar Sani Danja ta shiga tsaka mai wuya (Bidiyo)

Fagbohun ya yi umurnin cewa dole wanda zai tsa masa ya kasance ma’aikaci kuma dole ya gabatar da shaidar dake nuna ya biya haraji na shekaru biyu zuwa ga asusun gwamnatin jihar Legas duk cikin sharrudan karban beli.

Ya daga sauraran karan zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel