Kudin makamai : Kotu ta sanya ranar da za ta cigaba da shari'a tsakanin EFCC da Dasuki

Kudin makamai : Kotu ta sanya ranar da za ta cigaba da shari'a tsakanin EFCC da Dasuki

Wata babbar kotu dake Maitama a Abuja, a yau din nan Talata 8 ga watan Oktoba, 2019 ta sanya ranar 11 ga watan Disemba a matsayin ranar da za ta saurari karar da hukumar EFCC ta shigar game da Kanal Sambo Dasuki mai ritaya tare da wasu mutum hudu a kan kudin makamai.

Jastis Hussein Baba Yusuf, alkalin dake jagorantar shari’ar ne ya dage karar bayan da ya saurari ta bakin lauyan hukumar EFCC, Mr Oluwaleken Atolegbe tare da abokin aikinsa Rotimi Jacob game da korar da suka shigar a kotun.

KU KARANTA:Yawan ‘yan Najeriya cikas ne ga cigaban kasar – Sarkin Kano

Dasuki wanda shi ne ya rike mukamin mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro lokaci mulkin Goodluck Jonathan, an kama shi ne tare da karamin ministan shari’a na waccan gwamnatin wato Ambasada Bashir Yuguda.

Haka kuma sauran mutanen da ake tuhuma a kan kudin makaman sun hada da, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, dansa Sagir da kuma kamfaninsa Dalhatu Investment Limited.

Ana zarginsu ne da laifuka 25 wadanda suka kunshi cin-amana da kuma facaka tare da handame dukiyar da yawanta ya kai N19.4bn.

A zaman na ranar Talata, lauyan hukumar EFCC, Oluwaleke Atolagbe ya shaidawa kotun cewa an dage karar ne domin sauraron hujjoji. Haka kuma ba za a iya cigaba da shari’ar ba saboda wanda ake tuhuma na farko bai halarci kotun ba.

Har ila yau, lauyan ya nemi bangaren da ke kariyar wanda ake tuhumar da su sake rubuta wata takardar neman izini ga kotu, saboda wadda su ka bayar a baya dauke ta ke da kwanan watan 3 ga Disemba.

A takaice dai abinda hukumar EFCC ke bukata daga garesu shi ne Dasuki ya kasance a farfajiyar kotu ranar 11 ga watan Disemba domin cigaba da shari’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel