An sa ranar cigaba da sauraron shari'ar Maryam Sanda da Bilyaminu Bello

An sa ranar cigaba da sauraron shari'ar Maryam Sanda da Bilyaminu Bello

- A yau Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke Maitama, Abuja ta sanya ranar cigaba da sauraron shari'ar Maryam Sanda da Bilyaminu Bello

- Ana zargin Maryam ne da laifin kisan mijinta har lahira

- Kotun ta saki tare da wanke mahaifiyarta, Maimuna Aliyu, dan'uwanta Aliyu Sanda da mai aikinta Sadiya Aminu

A yau Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke Maitama ta sanya 16 ga watan Oktoba don sauraron shari'ar Maryam Sanda, matar da ake zarginta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

Mai shari'a Yusuf Halilu ne ya dage sauraron karar.

Ana zargin Maryam ne da kisan Bilyaminu, marigayin mijinta kuma dan tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Bello Muhammad a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2017.

KU KARANTA: Fushin naki aminta da soyayyarsa ta sa ya watsa min acid a fuska, in ji Rangoli

Kotun ta sallami mahaifiyar Maryam, Maimuna Aliyu, dan'uwanta, Aliyu Sanda da kuma mai aikinta, Sadiya Aminu, da ake zarginsu da taimakawa Maryam wajen boye shaidar kisan mijinta ta hanyar goge jininsa a inda ta caka masa wuka.

'Yan sandan sun ce laifin ya ci karo da tanadin sashi na 221 na Penal Code.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, a ranar 4 ga watan Afirilu, Jastis Halilu ya yanke hukuncin cewa, akwai bukatar Maryam ta gurfana akan tuhumar da ake mata. A don haka ne yace ta shigar da kariyar kanta.

Masu kara sun gabatar da shaidu 6 don tabbatar da zargin da ake wa me kare kanta.

Halilu ya bada umarnin Maryam ta fara kare kanta tare da saki da wanke mutane uku ganin cewa 'yan sandan sun kasa danganta laifin da suke zarginsu da wadanda ake zargin.

"Na umarci wacce ake kara da ta kare kanta akan laifin kisan kai da ake zarginta da shi wanda kuwa hukuncinsa kisa ne," in ji mai shari'a Halilu.

A lokacin, alkalin ya dage sauraron shari'ar zuwa 6 ga watan Mayu kuma ya yi umarnin cewa za a cigaba da sauraronta ne kullum sai dai ko idan kotun ta bada umarni sabanin hakan.

Ba a iya cigaba da shari'ar ba saboda alkalin yana sauraron karar zaben jihar Ogun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel