Wadume: Akwai hannun sojoji da dan sanda a kisan 'yan sanda uku - Kwamitin bincike

Wadume: Akwai hannun sojoji da dan sanda a kisan 'yan sanda uku - Kwamitin bincike

Kwamitin da aka kafa domin gudanar da bincike a kan kisan jami'an 'yan sanda uku da farar hula biyu a cikin watan Agusta a jihar Taraba ya samu rundunar 'yan sanda da ta soji da laifi a kan batun kisan mutanen biyar.

A cikin jawabin da hedikwatar rundunar tsaro ta kasa ta fitar ranar Talata, ta ce kwamitin ya gano cewa an samu matsalar sadar wa a tsakin jami'an 'yan sanda da suka kamo mai garkuwa da mutane, Bala Hassan 'Wadume', da sojojin da ke aiki a wani shingen duba ababen hawa a cikin jihar Taraba.

Dakarun soji sun kashe jami'an 'yan sanda uku da ke aiki da rundunar PIR (police intelligence response) yayin da suke kan hanyarsu ta koma wa Jalingo bayan sun kamo Wadume daga karamar hukumar Ibbi a ranar 6 ga watan Agusta.

Sojojin sun bude wa motar jami'an tsaron wuta, sannan sun saki mai laifin da 'yan sandan suka kamo.

Kazalika, karin wasu mutane biyu, farar hula, da ake kyautata zaton suna aiki tare da jami'an 'yan sandan, sun rasa ransu bayan sojojin sun bude wa motar 'yan sandan wuta.

Batun kisan jami'an ya fusata rundunar 'yan sanda, lamarin da yasa ta zargi sojoji da kai wa jami'anta hari da gan-gan domin su kubutar da mai laifi.

DUBA WANNAN: Manyan ma'aikatu 10 da Buhari ya ware wa makudan biliyoyi a kasafin 2020

Rahotannin kafafen yada labarai sun tabbatar da cewa akwai wata alaka mai cike da ayoyin tambaya a tsakanin kasurgumin mai garkuwa da mutane, Wadume, da wani babban soja, Kaftin Tijani Balarabe.

Kazalika, wani bincike da rundunar 'yan sanda ta gudanar ya gano cewa Wadume na yawan yin waya da wasu manyan jami'an 'yan sanda a karamar hukumar Ibi, inda aka kama shi.

Kwamitin ya bukaci a kara zurfafa bincike a kan Kaftin Balarabe da Wadume tare da wasu manyan 'yan sanda hudu da kuma dan sanda mai binciken laifuka a ofishin rundunar na karamar hukumar Ibi.

Wadanda kwamitin ya umarci a gurfanar a gaban kwamitin ladabtarwa sun hada da; Kaftin Tijani Balarabe, Saja Ibrahim Mohammed, Kofur Bartholomew, ASP Aondoona Iorbee da Insifekta Aliyu Dadje.

Ibikunle Olaiya, babban sojan sama, shine ke jagoranatar kwamitin dake da wakilai daga hedikwatar tsaro, rundunar sojin kasa, rundunar sojojin ruwa, rundunar 'yan sanda, DSS da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel