Yan majalisa kuyi hakuri, ina fama da mura sakamakon namijin aiki - Buhari

Yan majalisa kuyi hakuri, ina fama da mura sakamakon namijin aiki - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyanawa yan majalisar dattawa da wakilai cewa su yi hakuri da muryarsa a jawabin da zai gabatar saboda yana fama da mura sakamakon namijin kokarin ya yi na ganin cewa ya kammala shirya kasafin kudin 2020.

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya fara gabatar da jawabinsa gaban yan majalisan inda yake bayyana kasafin kudin 2020.

Yace: "Ku yi hakuri da murya na. Kamar yadda kuke gani ina fama da mura sakamakon namijin kokarin da nayi domin gabatar da kasafin kudin nan."

Mun kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya isa majalisar domin gabatar da kasafin kudin Najeriya ta shekarar 2020.

Daga shigansa, wasu yan majalisan suka fara yi masa ihun oyoyo baba.

Shugaba Buhari ya zauna kafin ya hau mimbari ya fara gabatar da jawabi. Gabanin haka, Sanata AbdulFatai Buhari ya yi addu'an Musulmai yayinda Hanarabul Nkiruka Onyeajeocha ta gabatar da adduar mabiya addinin Kirista.

Daga nan, sai shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya gabatar da jawabin maraba ga shugaba Buhari zuwa zauren majalisar karo na farko na majalisa ta tara.

Sanata Ahmad Lawan ya bayyanawa shugaba Buhari cewa majalisar shriya take da baiwa gwamnatinsa goyon baya wajen aiwatar ayyukanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel