Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira majalisar dokokin tarayya

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira majalisar dokokin tarayya

Labarin da muke kawo muku kai tsaye daga majalisar dokokin tarayya dake Abuja shine shugaba Muhammadu Buhari ya isa majalisar domin gabatar da kasafin kudin Najeriya ta shekarar 2020.

Daga shigansa, wasu yan majalisan suka fara yi masa ihun oyoyo baba.

A yanzu haka, shugaba Buhari ya zauna kafin ya hau mimbari ya fara gabatar da jawabi.

Gabanin haka, Sanata AbdulFatai Buhari ya yi addu'an Musulmai yayinda Hanarabul Nkiruka Onyeajeocha ta gabatar da adduar mabiya addinin Kirista.

Daga nan, sai shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya gabatar da jawabin maraba ga shugaba Buhari zuwa zauren majalisar karo na farko na majalisa ta tara.

Sanata Ahmad Lawan ya bayyanawa shugaba Buhari cewa majalisar shriya take da baiwa gwamnatinsa goyon baya wajen aiwatar ayyukanta.

Mun kawo muku rahoton cewa Jami'an tsaro sun mamaye majalisar dokokin tarayya yayinda suke shirin karban bakuncin shugaba Muhammadu Buhari inda zai gabatar da kasafin kudin 2020 yau Talata, 8 ga watan Oktoba, 2019.

Da misalin karfe 6 na safen nan, jami'an tsaro sun mamaye kofar shiga majalisa inda suke hana duk marasa takardar shiga wucewa.

An hana wasu Ma'aikatan majalisar da yan jarida maras katin shiga majalisa wucewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel