Kuma dai: An sake garkuwa da mutane 4 yayinda aka kashe mutum 1 a kauyen Kaduna

Kuma dai: An sake garkuwa da mutane 4 yayinda aka kashe mutum 1 a kauyen Kaduna

Yan bindiga sun halaka wani mutum da aka ambata da suna Mista Ezra Haruna yayinda suka yi garkuwa da wasu hudu a safiyar ranar Litinin a Anguwan Barau, garin Udawa, a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa yace an sace mutanen guda hudu ne a lokacin da yan bindigan suka isa garin da misalin karfe 4:00 na asubahin ranar Litinin sannan suka fara harbi.

Yace a lokacin da mutane suka ji harbe-harben bindigan sai suka fara gudu zuwa bangarori daban-daban sannan a cikin haka ne mutum daya ya mutu.

Sunayen wadanda aka sace sune Misis Jummai Ido, matar fasto din cocin Godiya Baptist Church, Angwan Barau Udawa; Mista Luka Auta, Mista Sale Auta da kuma Mista Yakubu Audu.

KU KARANTA KUMA: An bayar da belin mutumin da ake tuhuma da lalata yar makwabcinsa mai shekara 7 kan N50,000

Kakakin yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, bai amsa kiran wayar da aka yi masa domin jin ta bakinsa akan lamarin ba.

A ranar Alhamis, anyi garkuwa da wasu dalibai mata shida da malamai biyu daga kwaleji a Kakaku Daji, karamar hukuma guda.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel