Sabbin salon hare-haren da 'yan ta'addan Boko Haram suka fito dasu

Sabbin salon hare-haren da 'yan ta'addan Boko Haram suka fito dasu

- Rikicin Boko Haram na kara ta'azzara yana komawa tamkar shekarun da suka gabata

- Bincike ya nuna karuwar rikicin duk da kuwa gwamnatin tarayya ta nuna cewa tuni ta fi karfin 'yan ta'addan

- A halin yanzu basu kaiwa mutanen gari hari, sun fi gane kaiwa jami'an tsaro, sojoji da kuma kayyayakin gwamnatin

Rikicin Boko Haram na kara ta'azzara yana komawa tamkar shekarun baya lokacin da 'yan ta'addan ke rike da wasu bangarori na arewa maso gabas, in ji rahoton SB Morgen.

Rikicin ya kai kololuwa ne a 2014 lokacin da 'yan ta'addan suka kama garuruwa da dama tare da kashe mutane masu yawa.

Kusan kananan hukumomi 21 a cikin 27 na jihar Barnon na karkashin 'yan ta'addan ne a 2014.

KU KARANTA: Kukah ya bayyana dalilin da yasa ake yiwa sarki Sanusi II bita da kulli

Gwamnati Najeriya ta yi ikirarin cewa ta fi karfinsu kuma ta nakasa su ta yadda baza su iya kwace wani yankin ba.

Amma rahoton SB Morgen, wata kafa bayanan sirri ta yankuna, ta ce, 'yan ta'addan dai na kara kwace wasu yankuna tare da kirkiro sabbin salon mallake yankunan arewa maso gabas din.

Rahoton ya ce, 'yan ta'addan sun rage kai farmaki ga mutane ne don su samu goyon baya tare da kara dakarunsu, amma kuma sun dage wajen harar jami'an tsaro.

Rahoton ya kara da cewa, hare-haren suna zuwa ne daga Boko Haram ta bangaren Shekau ne, wacce har yanzu take cin karenta babu babbaka a yankin kudancin Barno.

"Wani dan majalisar wakilai daga jihar Barno ya yi ikirarin cewa, Boko Haram na rike da kananan hukumomi 8 na jihar," in ji rahoton.

"Koda kuwa akwai yuwuwar fadin ba daidai ba, rahoton da kungiyoyin taimakon kai da kai tare da mazahna jihar, sun tabbatar da cewa 'yan ta'addan na yawo ba tare da wani kalubale ba a kauyukan jihar. Wannan kuwa shaida ce akan harin kwanan nan da aka kai hedkwatar kananan hukumomo inda 'yan ta'addan suka kwashe kayan shaguna tare da taba kayan gwamnati." Rahoton ya kara

Kamar yadda rahoton ya nuna, jami'an tsaro, matsayar sojoji da kayan gwamnati su ne kawai 'yan ta'addan suke kaiwa hari.

Duk da kuwa hare-haren sun kai kololuwa a 2015, an samu ragowa a 2108 amma kuma an samu cigaba a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel