Majalisar zartarwa tayi na’am da karin N727b a kasafin kudin 2020

Majalisar zartarwa tayi na’am da karin N727b a kasafin kudin 2020

Majalisar zartarwa a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, ta amince da Karin naira biliyan 727 da majalisar dokokin tarayya tayi a cikin naira triliyan 10.2 na rabe-raben kasafin kudin.

Bayan ganawar sa’o’i biyar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, majalisar zartarwan ta amince da naira tiiliyan 10.729 da bangaren dokoki ta dawo mata dashi.

An tattaro cewa majalisar, a taronta na ranar Litinin, ta amince da kasafin kudin 2020 wanda Shugaban kasar zai gabatar a gaban majalissun hadin gwiwa na dokokin tarayya.

Wata majiya, wacce ta nemi a boye sunanta tace, majalisar zartarwar ta yaba ma majalisar dokoki akan karin kudin danyen mai daga $55 zuwa $57 kowace ganga.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni sun tabbatar da rikicin cikin gida a jam’iyyar APC

A wani lamari na daban, mun ji cewa Jami'an tsaro sun mamaye majalisar dokokin tarayya yayinda suke shirin karban bakuncin shugaba Muhammadu Buhari inda zai gabatar da kasafin kudin 2020 yau Talata, 8 ga watan Oktoba, 2019.

Da misalin karfe 6 na safen nan, jami'an tsaro sun mamaye kofar shiga majalisa inda suke hana duk marasa takardar shiga wucewa. An hana wasu Ma'aikatan majalisar da yan jarida maras katin shiga majalisa wucewa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel