Shikenan Kwankwaso ya samu kishiya a Kano: Wani dan majalisa zai kai dalibai 100 kasar turai karatu

Shikenan Kwankwaso ya samu kishiya a Kano: Wani dan majalisa zai kai dalibai 100 kasar turai karatu

- Alamu na nuni da cewa tsohon Sanata Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya samu kishiya a Kano

- Yayin da wani dan majalisa ya kuduri aniyar tallafawa dalibai 100 domin suje kasar turai su yi digiri na farko

- Tuni dai har an fara bawa matasa wannan fom da zasu cika domin fara tantance wadanda suka cancanta a kai kasar ta Chana da Sudan

Bayan wasu maganganu da suka bulla a 'yan kwanakin nan kan cewa shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya Hon. Sha'aban Ibrahim Sharada ya dauki nauyin kai dalibai 100 kasashen ketare, jaridar Dabo FM ta bi diddigin yadda wannan lamari yake.

A yadda jaridar ta bayyana, wani makusanci ga dan majalisar mai suna Hon Ibrahim Rabiu Tahir, wanda yake wakiltar karamar hukumar birni, ya tabbatarwa da jaridar cewa kwarai akwai wannan magana.

Hon Ibrahim Rabiu Tahir dai shine shugaban kasuwar Beruit dake jihar ta Kano, wanda ya fito takarar majalisar tarayya a zaben da ya gabata, ya kara da cewa: "Kwanakin da suka gabata ma munyi wata ganawar sirri akan wannan hobbasa tare da mutanen da muka dauka su zabi wadannan dalibai."

"Yanzu haka bana gari bayan wani rashi da aka yi mini, amma ina tabbatar muku da cewa abubuwa sun riga sun yi nisa, kuma zan sanar daku duk abinda ake ciki da zarar na dawo gida."

An gano cewa dan majalisar ya raba fom ga mutanen dake mazabar shi, kuma har wasu daga cikinsu sun cika wannan fom din sun mayar dashi domin a tantance su.

KU KARANTA: Ina nan da raina ban mutu ba - Fakhriyya ta fito ta karyata maganar mutuwarta

Haka kuma a wani rahoto da jaridar Leadership ta fitar ta bayyana cewa mai taimakawa dan majalisar, Faruk Malami Sharada ya shaida wa jaridar cewa dan majalisar yayi rabon fom ga matasan.

Ya ce, dan majalisar ya gama shiryawa tsaf domin bada tallafin karatu ga matasa 200 da zai tura kasar Sudan da China.

Ya kara da cewa an bayar da wannan fom domin tantance mutane 100 su je su yi karatun digiri na farko a bangaren kimiyya da fasaha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel