An sake kwatawa: An sake nuno gwamnan Ganduje yayi likimo yana sharar bacci a wajen taron da ya raka Buhari kasar Afrika ta Kudu

An sake kwatawa: An sake nuno gwamnan Ganduje yayi likimo yana sharar bacci a wajen taron da ya raka Buhari kasar Afrika ta Kudu

- Wasu hotuna da suke yawo a kafafen sadarwa sun nuna yadda gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kwantar da kai yana sharar bacci a wajen taro

- Hotunan dai an dauke su ne a wajen wani taron da gwamnan ya raka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasa Afrika ta Kudu

- Dama can dai gwamnan jihar yayi kaurin suna wajen irin wannan bacci a wajen taro

Wani sabon hoto na gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yadu a shafukan sada zumunta, inda aka nuno shi yana bacci hadda minshari a wajen wani taro da suka halarta shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar Afrika ta Kudu.

Gwamna Ganduje dai yayi wannan tafiyar ne da shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Larabar nan, wata ziyara da shugaban kasar ya kai kasar Afrika ta Kudu, domin bin kadi akan kisan 'yan Najeriya da ake yi a kasar Afrika ta Kudu.

A lokacin ziyarar, gwamnatin Najeriya ta hadu da gwamnatin kasar Afrika ta Kudu domin su samo masalaha dangane da kashe 'yan Najeriya da ake yi a kasar ta Afrika ta Kudu.

KU KARANTA: Ina nan da raina ban mutu ba - Fakhriyya ta fito ta karyata maganar mutuwarta

A yayin da ake gabatar da wannan taron ne aka hango gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje yana sharar bacci hadda minshari.

Idan ba a manta ba makonnin da suka gabata ne 'yan kasar Afrika ta Kudu suka dinga bi suna kashe baki mazauna can suna bankawa shagunansu wuta bayan sun debe kayan ciki.

Wannan dalili ne ya sanya gwamnatin Najeriya ta nemi duka 'yan Najeriya mazauna can da su dawo gida Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel