Hada ilmin Boko da Tsangaya: Gwamnatin Kano ta dauki malamai 600 da zata tura makarantun almajirai 393

Hada ilmin Boko da Tsangaya: Gwamnatin Kano ta dauki malamai 600 da zata tura makarantun almajirai 393

A cikin yunkurin hada ilmin Boko da tsangaya a jihar Kano, gwamnatin jihar ta dauki sabbin malaman sa kai 600 domin tura su makarantu 393 dake kananan hukumomi 44 na jihar.

A cewar gwamnatin, sabbin malaman za su karantar da ilmin yaren Turanci da Lissafi a ranakun Alhamis da Juma'a a makarantun tsangaya da ke jihar domin inganta ilmin almajiran.

Wannan mataki da gwamnatin ke dauka wani shiri ne na tabbatar da cewa yan makarantun tsangaya sun samu ilmin Boko da zai basu daman cigaba da karatunsu a gobe.

Gabatar da takardun daukan aiki ga malaman a gidan gwamnatin jihar, gwamna Abdullahi Ganduje wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Dakta Kabiru Shehu, ya ce wannan na daya daga cikin matakan aiwatar da shirin ilimi kyauta kuma wajibi na gwamnatin nan.

KU KARANTA: An karfafa tsaro a majalisa yayinda Buhari zai gabatar da kasafin kudin kasa yau

Yace: "Wannan na tabbatar da shirin gwamnati na tabbatar da cewa an samar da ilimi ga kowa, kyauta kuma wajibi."

"Wannan taro na yau kaddamar da shirin koyar da yara ne wanda BEDA ke bada gudunmuwa domin taimakawa wajen samar da ilimi ga kowa."

Ya kara da cewa gwamnatin ta yanke shawaran dauka malamai 3000 domin ingantan shirin hada ilmin da Boko da tsangaya a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel