Kukah ya bayyana dalilin da yasa ake yiwa sarki Sanusi II bita da kulli

Kukah ya bayyana dalilin da yasa ake yiwa sarki Sanusi II bita da kulli

- Mathew Kukah, Shugaban majami'ar katolika dake Sokoto, ya ce Sarki Sanusi II na maganganun da yake ne don kare karagarsa

- Babban malamin mabiya addinin kiristan ya sanar da hakan ne a ranar litinin yayi jawabinsa da ya yi a taro na 25 na kungiyar tattalin arzikin Najeriya

- Babban malamin ya ce kamata yayi gwamnati ta sa ilimi a sahun farko kafin wani batu na tattalin arziki ya biyo baya

Mathew Kukah, yace Muhammadu Sanusi II, sarkin Kano, na fada ne don rike karagarsa.

Malamin ya yi wannan jawabin ne a ranar litinin yayin taro karo na 25 na NESG.

"Sarkin yana nan yana fadar gaskiya. Hakan kuwa yasa ake hangensa a wata matsaya. A dalilin hakan ne abun ya zama wata magana daban," in ji shi.

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya murkushe rinjayen Sanusi ta hanyar kirkiro masarautu hudu masu daidai iko irin na Sarkin.

KU KARANTA: Alheri danko: An karrama DPO da ta biyawa wani kudin asibiti

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, matsalar basaraken da Ganduje na da alaka ne da kalubalantarsa da ya dinga yi a 2017 akan baiwa kamfanonin kasar China kwangilar gwamnatin jihar da kuma yawon gwamnan zuwa kasashen ketare.

A yayin magana kan halin da bangaren ilimi na jihar ke ciki, Kukah yace gwamnoni na kashe kudi akan hajji da gina wajajen bautawa a maimakon habaka bangaren ilimi.

"Kudaden da ke fitowa daga bangaren zuwa jihohinmu, na waye? A duk lokacin da aka ce ba za a habaka bangaren ilimi ba, toh gaskiya ana kyankyasar kiyayya ne,"

Ya kara da cewa, "Idan ka dubi arewacin Najeriya, inda babu mace ko daya a majalisar jihohi ko ta dattawa, mai sa'a ce kawai ke zama kwamishinan harkokin mata. Gwamnatin tarayya dama tace bata da hurumin magana ga jihohin nesa inda gwamnonin basu mutunta ilimi."

Kukah, da yayi ikirarin yana da makarantun sakandire 5, ya ce 60% na daliban makarantun nasa musulmai ne.

"Na mallaki makarantun sakandire 5 kuma na dogara ne da kudin da ake tarawa a majami'a don kula da su. Kashi 60 na daliban duk musulmai ne. Zan samu damar tattaunawa da gwamnatocin jihohi? Amsar itace a'a." In ji Kukah.

"Abinda nake so ku gane shi ne, arewacin Najeriya na taka rawar gani lalata abubuwa da dama. Ina fadar hakan ne da asalin gaskiyata." a cewarsa.

Malamin ya ce, yakamata Najeriya ta fara iya mulkar banbance-banbancen mutanen kasar kafin kokarin habaka kasar don nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel