Gwamnoni sun tabbatar da rikicin cikin gida a jam’iyyar APC

Gwamnoni sun tabbatar da rikicin cikin gida a jam’iyyar APC

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a lokacin wani ziyarar bangirma tayi kira ga shugabancin majalisar dokokin tarayya na tara a Abuja a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, tayi korafi akan rashin hadin kai tsakanin zababbun mambobin majalisar zartawa da na majalisar dokoki.

Gwamnonin na APC sun samu jagorancin shugabansu, Atiku Bagudu na jiha Kebbi zuwa majalisar, sannan sun samu tarba daga shugabancin majalisar dokokin na tara karkashin jagorancin Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Bagudu ya bayyana cewa sun zo majalisar dokokin kasar ne domin su gabatar da rahoton kwamitin kungiyar akan lamuran majalisar dokoki, wanda Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari.

Da yake jawabi a taron, Masari yayi korafin cewa duk kokarin da kwamitinsa tayi domin ganin an samu kyakyawar alaka tsakanin gwamnoni da majalisar dokokin tarayya bai cimma sakamakon da ake so ba.

KU KARANTA KUMA: Yadda mu ka gyarawa Gwamnonin da ke facaka zama a Najeriya - Magu

Ya bayyana cewa rashin hadin kai tsakanin zababbun yan majalisa na jiha da yan majalisar tarayya ya haifar da rikici wanda ka iya tarwatsa jam’iyyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel