Alheri danko: An karrama DPO da ta biyawa wani kudin asibiti

Alheri danko: An karrama DPO da ta biyawa wani kudin asibiti

- Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya karrama DPO din ofishin 'yan sanda dake Ogudu

- Ya jinjina mata ne sakamakon aikin jin kai da ta bayyana

- Ta kwashi wani maraya da 'yan fashi suka harba tare da kaisa asibiti har da biya masa kudin asibiti

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya karrama DPO din ofishin 'yan sanda da ke Ogudu sakamakon tallafawa wani wanda aka yi wa fashi da makami da tayi.

Sanwo-Olu ya kwatanta Celestina Kalu da 'Dan sanda abokin kowa', gani da yadda ta tseratar da rayuwar maraya, Friday Ajabor.

Ajabor, matashi mai shekaru 25 kuma maraya daga jihar Edo, na tare da abokinsa a Ojota wajen karfe 8 na yamma a ranar 19 ga watan Satumba, lokacin da 'yan fashi biyu suka zo don musu fashi.

KU KARANTA: Wani gwamnan PDP ya yi nasara a kotun sauraron kararrakin zabe

Abokin Ajabor ya samu ta tsere bayan artabun da suka sha da 'yan fashin inda ya bar Ajabor tare dasu.

Fushin fadan da suka yi dasu yasa suka harbi Ajabor tare da tserewa.

Rundunar 'yan sanda daga ofishinsu na Ogudu sun isa wajen inda suka tarar da Ajabor cikin jini.

'Yan sandan sun kwashesa zuwa asibitoci har biyu inda aka ki karbarsa sakamakon rashin gado. Bayan kusan mintuna 90 aka karbesa a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas. Kalu ta cire kudinta tare da biya masa duk kudin da asibiti suka cajesu.

Kokarin jami'ar 'yan sandan ya tseratar da rayuwar marayan saboda an kasa samun 'yan uwansa.

Hali nagari irin na jami'ar 'yan sandan ne ya jawo hankalin gwamna Sanwo-Olu bayan da aka dinga yadawa a shafukan sada zumunta.

Hakan ne kuwa yasa gwamnan ya nemi 'yar sandar tare da karramata.

Gwamnan ya ce, "Jami'ar yan sandan ta nuna hali nagari da ya dace na baya suyi koyi da ita. Ina horon jami'an tsaro da su kwaikwayi halin da ta bayyana wajen aikata abinda ba nauyinta bane. Wannan na daga cikin halayyar shugaban nagari. Kwatanta taimako koda kuwa ba daga cikin aikinka yake ba."

"Ba wai taimako kadai ba, ta kara da biya masa kudin asibiti wanda zamu ce kwalliya ta biya kudin sabulu tunda marayan na nan da ransa." cewar gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel