Yanzu yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 9 a Abuja

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 9 a Abuja

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da mutane tara, ciki harda yaro dan shekara 12 a garin Pegi, da ke yankin Kuje a babbar birnin tarayya Abuja.

Yan bindiga sanye da kayan sojoji ne suka yi garkuwa da mutanen a daren ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, da misalin karfe 8:00 na dare.

Yan bindigan sun harbi motoci biyu, da suka hada da NISSAN Frontier da Toyota Solara.

Harsashin ya fatattaka tayoyin, inda ya yi ramunmuka a jikin motocin.

An tattaro cewa daya daga cikin wadanda abun ya cika dasu na a cikin mawuyacin hali.

Wani da abun ya cika dashi wanda aka saka akan dalili na rashin lafiya yace maharani ba za su yi kasa da 20 ba.

KU KARANTA KUMA: An bayar da belin mutumin da ake tuhuma da lalata yar makwabcinsa mai shekara 7 kan N50,000

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu garkuwa da mutanen sun kira da safiyar yau Talata, 8 ga watan Oktoba inda suka bukaci yan uwan wadanda aka sace su biya naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa.

Wannan shine karo na biyu da lamarin gakuwa da mutane ke faruwa a garin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel