An bayar da belin mutumin da ake tuhuma da lalata yar makwabcinsa mai shekara 7 kan N50,000

An bayar da belin mutumin da ake tuhuma da lalata yar makwabcinsa mai shekara 7 kan N50,000

Rundunar yan sanda a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, ta gurfanar da wani dan shekara 25, Ibrahim Musa, a gaban kotun Mararaba, da ke zama a jihar Nasaawa kan zargin lalata yar makwabcinsa mai shekara bakwai a duniya.

Sai dai kuma kotu ta bayar da belinsa akan kudi naira 50,000 bayan yaki amsa tuhumar da ake masa.

Ana shari’a da Musa wanda ke zama a Mararaba, Nasarawa akan zargin cin zarafin karamar yarinya, amma dai ya karyata aikata laifin.

Dan sanda mai kara, Sajen Godwin Ejeh, ya fada ma kotu cewa mai karar, Misis Thomas, a ranar 26 ga watan Yuli ta kai rahoton lamarin ga ofishin ya sanda, Mararaba.

A cewar Ejeh, mai karar tayi zargin cewa wanda ake karar ya yaudari yarta mai shekara bakwai sannan yayi zina da ita.

KU KARANTA KUMA: Yadda mu ka gyarawa Gwamnonin da ke facaka zama a Najeriya - Magu

Alkalin, Ibahim Shekarau, ya bayar da belin wanda ake karan kan kudi N50,000 tae da wanda zai tsaya masa mutum daya sannan ya dage sauaron karan zuwa ranar 16 ga watan Oktoba.

An faa ambaton lamarin ne a watan Agusta lokacin da aka ki bayar da belin wanda ake tuhuma inda aka tsare shi a gidan maza da ke Keffi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel