Yadda mu ka gyarawa Gwamnonin da ke facaka zama a Najeriya - Magu

Yadda mu ka gyarawa Gwamnonin da ke facaka zama a Najeriya - Magu

Mukaddashin Shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu, a jiya Litinin, 7 ga watan Oktoba, yace karfin rashawa a Najeriya bai kai yadda yake ba a baya.

Magu a wata hira da manema labarai a Makurdi, lokacin ziyarar da ya kai ofishin hukumar, ya kuma bayyana cewa a yanzu gwamnoni na taka-tsantsan sosai wajen halartar kasaitattun bukukuwa a gida da waje.

“Ba a yiwa rashawa ganganci kamar yadda ake yi a baya. Hatta gwamnoni tsoron halarta kasaitattu bukukuwa suke yi a gida da wajen kasar. Baya faruwa a yanzu. Akwai wannan tsoron,” inji shi.

Shugaban na EFCC ya kara da cewa ya zo Makurdi ne, domin ya tattara dukkanin mazauna jihar Benue kan su yaki rashawa, inda ya kara da cewa akwai bukatar kowa ya kasance a cikin yakin domin fatattakar rashawa daga tsarin kasar.

KU KARANTA KUMA: CCB: Dalilin mu na kin fito da dukiyar Shugaban kasa Buhari da Yemi Osinbajo fili

Ya bayyana cewa ba tare da la’akari da siyasa ba, hukumar a karkashin kulawarsa za ta bi ta kan duk wanda aka kama da laifi sannan za ta tabbata da ya fuskanci hukunci.

Yace a yan kwanakin nan EFCC ta gurfanar da masu laifi da dama a fadin jihohi 13 da take aiki a kasa sannan cewa ana cigaba da kama mutane da dama da ke damfara ta yanar gizo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel