CCB: Dalilin mu na kin fito da dukiyar Shugaban kasa Buhari da Yemi Osinbajo fili

CCB: Dalilin mu na kin fito da dukiyar Shugaban kasa Buhari da Yemi Osinbajo fili

Shugaban hukumar CCB mai sa-ido a kan kadarorin ma’ikatan gwamnati a Najeriya, ya yi bayani game da abin da zai hana su bayyana abin da shugaban kasa da Mataimakinsa su ka mallaka.

Mohammed Isah ya yi karin haske ne a kan dalilinsu na kin fadawa Duniya diddikin kadarori da dukiyar shugaba Muhammadu Buhari da kuma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

A lokacin da Isah yake zantawa da Manema labarani Ranar 7 ga Oktoba kamar yadda NAN ta rahoto, ya bayyana cewa majalisar tarayya ba ta sa sharadin a yi hakan ba duk da rokon da ake yi.

A cewar shugaban hukumar ta CCB, su na aiki ne da dokar tsarin mulki da dokar FOI a matsayin madogara. Mohammed Isah yace ko da wani ya bukaci samun wannan bayani sai an bi ka’ida.

Isah yace sakin layi na uku na dokar tsarin mulkin Najeriya ya ba CCB damar boye bayanai kan kadarori da dukiyar da ma’aikacin gwamnati ya mallaka har sai majalisa ta yi na’am a ba wani.

KU KARANTA: Wasu tsirarrun mutane sun tattara dukiyar Najeriya - Buhari

“Saboda haka idan wani mutum a kan-kin kansa ko kuma kungiya ta na son samun bayani kan dukiyar wani jami’i, dole sai an cika duka sharudan da dokar FOI ta gindaya.” Inji Mista Isah.

Duk da wannan bayani da shugaban hukumar ya yi, bai nuna alamun ya nemi majalisa ta fito da sharudan ba. Bai kuma bayyana ko su na da shiri nan gaba na ganin majalisa ta yi hakan ba.

Dokar FOI ta ba kowane ‘dan kasa samun kowane irin bayani a gwamnatin Najeriya muddin bai shafi bangaren tsaro ba. Wannan ya sa kotu ta ba wasu damar sanin abin da Buhari ya mallaka.

A baya dai hukumar ta ba wani tsohon Hadimin shugaban kasa Buhari bayanai a game da kadarorin Walter Onnoghen wanda wannan bincike ya na cikin abin da ya sa Alkalin ya bar ofis.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel